Yadda Suwaiba ta kashe budurwar mijinta Aisha saura sati daya su yi aure a Kano

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wata matar aure mai suna Suwaiba Shuaibu dake da shekaru 20 da ake zarginta da laifin kashe budurwar mijinta Aisha Kabir mai shekaru 17.

Kakakin rundunar Abdullahi Kiyawa ya tabbatar da aukuwar wannan mummunar abu yana mai cewa Suwaiba ta caka wa Aisha wuka a wani kangon gini ana sauran sati daya ta auri mijinta a matsayin mata ta biyu.

Abdullahi ya ce wani Kabiru Jafaru ne ya kai kara ofishinsu cewa Aisha ta bace.

“Suwaiba ta kashe Aisha saboda tsananin kishin mijinta Shuaibu Ali zai aure ta.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Habu Sani ya bada umurnin aikawa da bayanan zargin kisan zuwa fannin da ake gurfanar da masu aikata laifuka irin haka domin ci gaba da bincike.

Ya ce da zaran an kammala za a kai Suwaiba kotu domin yanke mata hukunci.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda wani mazaunin kauyen Dakaiyawa dake karamar hukumar Kaugama, jihar Jigawa, ya daba wa saurayin tsohuwar matar sa wuka da yayi sanadiyyar rasuwar sa saboda tsananin kishi.

Tsohon mijin mai suna Umaru ya bi saurayin tsohuwar matarsa har inda yake, sannan ya caka masa sharbebiyar wuka saboda tsananin kishin wai yana tadi da ita, duk da ya sake ta.

An gano cewa, Umaru ya saki matar sa da kwana uku sai sabon saurayi ya bayyana, ashe hirar ajali yake yi.

Share.

game da Author