Yadda gobara ta yi ta’adi a Makarantar Sojoji ta Zaria

0

Gobarar da ta tashi a Makarantar Horas da Kuratan Sojoji da ke Zaria ta lalata wasu sassa da kayayyakin makarantar.

Makatarantar mai suna (Nigerian Army Deport Zaria), ta na a Zaria ne cikin Jihar Kaduna.

Ba a samu asarar rai ko daya a gibarar ba.

A wannan makaranta ce ake horas da kananan sojojin da a Hausance ake kira kuratan sojoji.

An gina makarantar tun cikin 1924, kuma har yau a cikin ta ne ake horas da kananan sojojin Najeriya.

Kwanan baya Babban Hafsan Sojojin Najeriya ya halarci wurin yi wa sabbin kuratan sojojin da ake dauka a Zaria, wani atisayen gwajin cancanta dauka aikin soja, a Dajin Fagore cikin Jihar Kano.

A lokacin Buratai ya shaida masu duk wanda aka dauka, to daga can za a zarce da shi makarantar da ke Zaria, domin ci gaba da horaswa.

Har ma ya kara da cewa, “kowanen ku ya shirya zuwa Dajin Sambisa. Duk wanda bai shirya zuwa Sambisa ba, to ya tattara komatsan sa ya koma gida kawai.”

A wannan makaranta ce aka samu tashin gobarar a Zaria.

Wani ganau ya shaida cewa wtar ta faro ne daga gidan kwanan sojoji mai lamaba Block 15, kuma ta tashi ne tsakar dare a ranar Asabar.

Har yanzu ba a samu an iya jin ta bakin jami’an da ya kamata su yi magana dangane da tashin gobar ba.

Share.

game da Author