Wani masani dabarun kiwon kifi, kuma Shugaban Tafkunan Kiwon Kifi na Aquatic Hub Afrique Network (AHAN), mai suna Steve Okeleji, ya bayyana cewa kasuwancin kiwon kifi a Najeriya na kara bunkasa, sai dai kuma duk da haka, ya bayyana cewa akwai bukatar zaburar da mutane domin kara samun jama’a masu tarin yawa da za su rungumi sana’ar kiwon kifaye hannu bibbiyu.
Ya ce idan aka yi hakan, za a kara samar wa matasa maza da mata masu tarin yawa aikin yi ta hanyar samun jarin kama sana’ar kiwon kifaye.
Cikin wata tattaunawa da ya yi da PREMIUM TIMES, Okeleji ya bayyana cewa akwai matukar bukatar gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi su shigo cikin lamarin, ta hanyar tallafawa domin a samar da aikin yi wajen bunkasa kiwon kifi a kasar nan.
“Idan har ana so a cimma adadin yawan kifin da ake so a rika samarwa a kasar nan, kamar yadda Hukumar Abinci Ta Majalisar Dinkin Duniya ta nemi a rika samarwa, to sai fa an tashi tsaye an kara samar da kimanin mutum 400,000 da za su kara shigowa cikin kasuwanci da kiwon kifi a kasar nan.”
Ya ce ai fannin kiwon kifi sana’a ce mai fadi da yawan gaske, wadda kwata-kwata duk da yawan masu sana’ar a ake gani kamar su na da yawa, to amma a gaskiya har yau babu ma wadatar mutanen da ake bukata a cikin sana’ar ta kiwon kifi.
Yayin da ake bukatar metric ton milyan 3.4 na kifi duk shekara a kasar nan, ya ce kashi 40 bisa 100 kadai na wannan adadin ake iya samarwa a cikin Najerfiya, sauran kuma duk daga waje ake shigo da su.
An kiyasta ana shigo da kifi akalla na fam milyan 625 a duk shekara a cikin kasar nan.
Ya ce farkon kalubalen da ya fara samu a sana’ar kiwon kifi uku ce, sama da shekaru 20 da suka gabata.
“Na fara fuskantar rashin wadatattu kuma kwararuun wadanda za su rika yin aikin kiwon kifin, kuma wadanda su ka san harkar sosai.
“Sannan na fuskanci rashin karfin jarin sana’ar, sai kuma matsalar kayan aiki ciki har da matsalar wutar lantarki. Kai ni fa har ma matsalar ruwan da zan yi kiwon kifin sai da na fuskanta.
“Amma cikin ikon Allah, tsakanin 2017 zuwa yanzu, mun kafa AHAN, inda mu ka bada horon dabarun kiwon kifi ga sama da mutum 3,500 maza da mata, matasa, dattawa da ma wadanda su ka yi ritaya daga aiki.”
Ya kara jaddada cewa Gwamantin Tarayya da ta Jihohi su bijiro sosai a cikin harkokin dabarun bunkasa kiwon kifi, ta hanyar bada lamunin kudade ga marasa karfi domin su rungumi harkar gadan-gadan har kasa samun masu kiwon kifi akalla mutum 400,000 a fadin Najeriya.
“Domin idan mu ka ce ana so a kai ga ka’idar Hukumar Abinci Ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO), to kenan ana bukatar mutum 400,000 kowa ya rika samar da kifaye 10,000 a shekara kenan.”