Kungiyar Kare Muradin Fulani Makiyaya, Miyetti Allah, ta yi kira a gaggauta kama dan rajin kafa kasar Yarabawa mai suna Sunday Igboho.
Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah na Jihar Oyo, Ibrahim Jiji ne ya bayyana haka ga manema labarai a Ibadan babban birnin Jihar, inda ya kara hakkakewa cewa Fulani makiyaya fa ba mabarnata ba ne.
“Dukkan mu dai ‘yan Najeriya ne. Mu na kaunar kokarin da Gwamnan Jihar Oyo Seyi Makinde ke yi wajen fitowa karara ya na fadin gaskiya. Mutanen mu ba su zaune lafiya, su na cikin tashin hankali, wasu ma sun gudu sun bar gidajen su.
“Mu na so a yi wa Sarkin Fulani adalcin dangane da barnar da aka yi masa a gida. Dukkan wadanda su ka yi masa barnar kona masa gidaje da dukiyoyi dole a kama su a hukunta su. Saboda ba su fi gwamnati karfi ba. Wane ne Sunday Igboho, kuma ta yaya aka yi har ya fi karfin gwamnati?
“Na sha fada cewa a cikin kowace kabila akwai mabarnata, ba wai sai a cikin Fulani kadai ba. Wadanda a yanzu ake gallazawa ba su ne masu laifin da ke addabar jama’a din ba. Wadanda ake kora a yanzu su ne fa ke zaune alfiya da mutane. Ya kamata gwamnati ta yi dukkan kokarin da za ta yi domin ta tabbatar zaman lafiya ya dawo a yankin Ibarapa.”
Shi dai Igboho shi ne ya ja zugar wasu matasa su ka kai wa Fulani farmaki a Ibarapa.
Sai dai kuma Kakakin Fadar Shugaban Kasa Garba Shehu, ya ce Shugaba Muhammadub Buhari ya umarci Sufeto Janar na ‘Yan sanda Mohammed Adamu ya sa a kama Sunday Igboho.
Sai dai kuma Kakakin Yan sandan Najeriya Frank Mba da na Jihar Oyo Olugbengba Fadeyi ba su amsa kiran PREMIUM TIMES ba, domin jin inda aka kwana.
Za A Yi Bala’i A Kasar Nan Idan Aka Kama Igboho – Matasan Yarabawa
Tuni da Yarabawa su ka tashi haikan a kungiyance su na cewa idan aka kama Sunday Igboho, to za a yi bala’i a kasar nan.
Haka shugaban kungiyar Matasan Yarabawa Olalekan Hammed ya bayyana.
Ya ce matasan yankin Ibarapa da ma wasu matasana Yarabawa ba za su bari a kama dan uwan su ba.
Discussion about this post