Yadda biyan tulin bashin da Najeriya ke ci ya hana kasafin kowace shekara tasiri ga talakawa

0

Najeriya za ta kashe kashi 1 bisa 4 na kasafin kudaden ta na 2021 wajen biyan basussukan da ake bi kasar.

Daga cikin kasafin naira tirliyan 13.58, naira tiriliyan 3.3 duk tafiya za su yi wajen biyan bashi.

Dama kuma a wannan skekara ce Buhari zai ciwo wasu sabbin basussuka har na naira titliyan 5.2.

Kasafin 2021 dai kenan kashi 24 din sa kudaden duk biyan bashi za a karkatar da su.

Kuma binciken ya nuna haka ke ci gaba da tafiya, tun daga 2016 har zuwa yanzu.

Cikin 2016 gwamnatin Buhari ta yi kasafin naira tiriliyan 6.6. amma kuma kashi 44 bisa 100 na kasafin, wato naira tiriliyan 1.5, duk a biyan bashi su ka tafi.

Shi ma kasafin 2017 na naira tiriliyan 7.3, an kashe naira titriliyan 1.6 wajen biyan bashi.

A 2018 an kashe naira tiriliyan 2.2 a wurin biyan bashi, daga naira tiriliyan 9.1 da aka yi na kasafin kudi.

Kasafin 2019 naira tiriliyan 8.9 ne, amma an biya bashin naira tiliyan 2.14 daga cikin kasafin.

Kasafin 2020 naira tiriliyan 10.3 ne, amma an biya bashi na naira tiriliyan 2.5 daga cikin kasafin.

Wani sharhi da aka buga a PREMIUM TIMES HAUSA ya yi dalla-dallar yadda kasafin zai kare wajen biyan bashi da kuma ciwo bashi.

Najeriya za ta shafe shekara daya cur ta na neman bashin naira tiriliyan 5.02, wadanda sai da su za a iya aiwatar da ayyukan kasafin 2021. Kenan kashi 40% bisa 100% na Kasafin naira tiriliyan 13.58 bashi ne za a ciwo, idan har ma an samu wanda zai bayar da bashin.

Kasashe manya su na yin kasafin su na shekara ta yadda zai amfani wasu kasashe masu yawa. Misali za a yi la’akari da me za a samar a ahekarar wanda wadancan kasashen tilas sai sun zo sun saya? Kamar makamai da sauran su.

A kasafin 2021 na Najeriya babu abin da za a samar wanda tilas sai Togo, Chadi, Ghana da sauran kasahen birjik sun shigo sun saya tilas.

Kasafin naira tiriliyan 13.58 ba wata tsiya ba ce a Kasa mai yawan al’umma kamar mutum milyan 200. Saboda darajar naira ta lalace a idon kudaden kasashen waje.

Cikin Naira biliyan 13.58, za a kashe naira tiriliyan 5 wajen biyan albashin Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (wato kashi 40% bisa 100% na kasafin).

Hakan na nufin daga cikin naira tiriliyan 7 da ake hasashen samu a matsayin kudin shiga, to naira bilyan 5 duk a biyan albashi za su tafi kenan.

Share.

game da Author