Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta kara gina sabbin gidajen kurkuku na zamani guda shida.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka a ranar Asabar a lokacin da ya kai ziyarar ganin yadda aikin ginin kurkukun Kano, wanda ake ginawa a Janguza ke tafiya.
Minista Aregbesola ya bayyana cewa aikin ginin kurkukun da ake yi a Karamar Hukumar Kumbotso a Janguza, ya na daga cikin shirye-shiryen aikin gyaran gidajen kurkukun kasar nan da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke gudanarwa.
Ya ce, “wadannan ayyukan ginin kurkuku da mu ke yi, su na daga cikin alkawurran da mu ka dauka kuma mu ke kan cikawa wajen gyaran gidajen kurkuku ta yadda za su tafi daidai da zamani.
“Wannan sabon gidan kurkuku da ake ginawa a Janguza, zai iya cin mutum 3,000. Kuma irin sa ne za mu sake ginawa a kowace shiyyar kasar nan shida.
“Wannan gidan kurkuku ya sha bamban da irin wadanda mu ka gada. Akwai wadatattun wurare da kuma wasu kayayyakin saukake kuncin zaman gidan kurkuku.
“Gaskiya na gamsu da irin yadda ginin ya ke da kuma irin yadda aikin ke tafiya.
Daga nan ya jinjina wa Shugaba Muhammadu Buhari a kan kokarin sa na gyaran gidajen kurkuku da kuma kokarin inganta rayuwar mazauna gidajen kurkukun.
Da ya ke magana da farko, babban kwanturola na Gidajen Kurkukun Najeriya, Ahmadu Jafaru, ya ce an tsara ginin kurkukun na Janguza har da makaranta a ciki da asibiti da wurin koyon sana’o’i da masallaci da sauran su.
Ya ce za a kammala ginin a cikin wannan shekarar. Ya kuma kara da cewa gwamnatin tarayya ta maida gidan kurkukun da ke Kurmawa a Kano gidan kula da marasa lafiyar da ke da wani musabbabi.
Discussion about this post