Yadda rikicin kabilanci ya gurgunta min sana’ar noma – Manomiya Susan

0

Wata rana a cikin 2013, Susan Godwin ta na zaune gidan ‘yar ta a Lafiya,babban birnin Jihar Nasarawa, ta na tsakiyar taya ta rainon jinjirin da ta haifa, sai aka kira ta, aka sanar da ita cewa rikicin kabilanci a Karamar Hukumar Obi ya yi sanadiyyar damka wa gidan wata tare da gonar ta, mai fadin hekta 30 wuta.

“ Daga kauyen mu wani ya kira ni a waya, ya shaida min cewa ana rikici, kuma ana ta banka wa gidajen wuta.” Haka Susan mai shekara 60 ta shaida wa PREMIUM TIMES yadda wannan rikici ya janyo mata tawaya Da koma-baya a harkokin noman ta.

Bayan rikici ya lafa, Susan da mijin ta da sauran yaran ta sun koma sun sake gina gidajen su, bayan shekara daya kuma sai aka sake kai masu hari. Tilas su ka sake tserewa daga garin na Obi.

“ Mun ga bala’i da idon mu. Saboda an kashe mutane da yawan gaske, barayi da makiyaya suka kwashe min amfani gona kakaf. Kuma su ka yi awon gaba da kayan aikin noman da ke cikin gonar’’.

“ Ni da ke da babban gona, sai ga ni na yi gudun hijira zuwa cikin Lafiya. A cikin 2015 Mai Unguwa ya ba ni hekta daya ta gona ya ce na noma.

“ Da yake gyada na yin albarka sosai a wurin, sai na sayi irin gyada na shuka. Na samu buhu takwas da na cashe ta.’’

Susan wadda mijin ta dan sanda ne, ta kama harkar noma gadan-gadan tun kafin rikici ya kassara harkar noman ta, saboda akwai albarka a fannin noma, kamar yadda ta shaida wa PREMIUM TIMES.

Bayan ta yi wani kwas din hororwa ne a Jos, sai ta koma cikin yankin karkarar su ta kama noma gandan-gadan, ta na noma doya, gyada, gero da kuma shinkafa.

Noma ya karbi Susan, har ta kan noma dubban doya, buhunan shinkafa daga 30 har zuwa 50 ta rika nomawa. Sannan kuma ta kan noma har buhu 40 na shinkafa mai nauyin kilogiram 50.

“ Akwai shekarar da na noma doya ta naira milyan 5, shinkafa ta naira milyan 1.2 sai masara ta naira 200,000 sai gero na naira 240,000. Na yi buhun kulikuli 16, inda na saida kowane buhu naira 18,000.”

Amma rayuwa ta canja wa Susan, noman da ta ke yi a Lafiya kadan ne, idan ta kwatanta da wanda ta rike yi a Tudun Adebu, garin su na haihuwa kafin rikici ya tarwatsa su.

Sai dai kuma ta ce su na shiryawa su koma kauye, domin su ci gaba da noman su. Ta kuma ce ko a can lafiya inda su ke a yanzu, su na cikin tsoron makiyaya, shi ya sa basu dadewa a wurin aiki a gonaki har tsawon lokaci.

Share.

game da Author