Sakamakon zaben kananan hukumomi da aka bayyana a Kano ranar Lahadi, shugaban hukumar zabe na jihar Kano, Ibrahim Garba-Sheka ya ce gaba daya kananan hukumomin jihar Kano 44 da kujerun kansiloli 484 duk APC ce ta cinyo su tas.
” Yan takara na jam’iyyar APC ne suka cinye zaben tas-tas. Duka kananan hukumomi 44 da kujerun kansiloli 484 duk APC ce ta lashe su tas, bata rage ko sidi.
Garba-Sheka ya zabe ya guna cikin lumana da kwanciyar hankali.
” Kuri’un da aka kada a zaben sun zarce miliyan biyu duk da ko ana ci gaba da karkare sauran ayyukan da ba a rasa bana zaben.
Sai dai kuma duk da wadannan nasarori da aka samu a wannan zabe da aka gudanar, kamar yadda Garba-Sheka ya karanto su, jam’iyyar PDP bangaren tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso ta janye daga fafatawa a wannan zaben.
Hakan bai hana bangaren PDP na Aminu Wali shiga zaben ba, sai dai ko Kansila daya cikin kansiloli sama da 400 da aka zaba basu ci ba.