Yadda mahara su ka kashe zaratan ’yan sandan ‘Mobal’ 4 a Kaduna a harin Kwanton-Bauna

0

Rundunar ’Yan Sanda ta Kasa ta tabbatar da kisan zaratan jami’an ta hudu da kuma bacewar guda daya, a wani kwanton-baunar da mahara su ka yi masu tsakanin Birnin Gwari da Funtua.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Kasa Frank Mba ya ce Sufeto Janar Mohammed Adamu ya jinjina wa zaratan jami’an tsaron, wadanda y ace na ‘Operation Puff Adder’ ne daga Kano.

Ya ce an tura su ne a cikin rundunar jihar Neja domin yin wani aikin fatattakar ’yan bindiga a dazukan Birnin Gwari, kuma sun je sun yi aikin su cikin nasara.

Sai dai kuma a kan hanyar su ta komawa Kano daga Birnin Gwari ne wasu mahara su ka yi masu kwanton-bauna.

An yi masu kwanton-bauna a cikin jihar Kaduna, daga Birnin Gwari kafin su kai Funtua.

“Ba gaskiya ba ne da ake cewa mahara sun sun yi garkuwa da jami’an tsaro 18. Hudu ne aka kashe ba 18 ba. Amma su ‘yan sandan sun yi nasarar kashe mahara birjik, sauran wadanda su ka gudu kuwa duk da raunukan harbi su ka tsere a cikin daji.

“Amma abin takaici an kashe ’yan sanda hudu, kuma dan sanda daya ba mu san inda ya ke ba har yanzu.”

Mba ya ce ‘yan sanda 16 ne aka yi wa kwanton bauna, amma hudu aka kashe, daya kuma har yanzu sun a kokarin ceto shi a cikin daji.

“Zaratan mu sun yi kokarin dauko gawarwakin jami’an da aka kashe. Kuma su na ta kokarin gano dan sanda daya da ba a san inda ya ke ba.”

Sufeto Janar Adamu ya yi ta’aziyyar jami’an da aka kashe su hudu. Ya na mai cewa za a tabbatar mutuwar su ba ta zama ta tafi a banza ba.

Tsakanin Birnin Gwari da Funtua na daya daga cikin dazukan da mahara ke neman hana matafiya wucewa, saboda yawan hare-hare da garkuwa.

Share.

game da Author