Kamfanin Dangote ya kammala titin Kankare na farko da Kamfanin ya yi a Najeriya.
Titin mai tsawon kilomita 43, ya ta so daga Obajana zuwa Kabba, a jihar Kogi.
Daraktan Ayyuka na kamfanin Olatunbosun Kalejaiye, ya ce yana matukar farin ciki da yadda ake gabatar da aikin ‘Corporate Social Responsibility Project’ don talakawan Najeriya wanda ta dalilin wannan shiri ne aka gina wannan titi.
Direbobi dake bin hanyar sun nuna jin dadin su suna masu cewa wannan hanya yanzu ita ce hanyar da aka fi idan za’a kudancin Najeriya daga Arewacin kasar nan.
Dangane da dimbin kudaden da aka yi amfani da su wajen gyaran hanyoyi, Shugaban Rukunin Dangote Aliko Dangote ya ce an shirya shirye-shiryen sauya hanyoyin Najeriya da kankare, yana mai jaddada cewa za a kai kayan da aka yi amfani da su wajen gyaran hanyoyi da kula da su zuwa wasu muhimman bukatun na. al’umma.
“Zamu gina manyan hanyoyi a cikin kasar nan ta yadda a duk lokacin da muka gina hanya, ba sai mun koma gyara ba bayan damina na shekara uku da yin hanuar. Irin wannan titi babu ruwansa da gyara ko kuma ramuka”.
Dangote ya ce maimakon a rika kashe makudan kudade don gyaran titi, idan aka yi irin wadannan hanyoyin a kasar nan, sai dai a kashe sauran kudaden da zuka rage a wasu harkokin ci gaban kasa.
A yayin bukin kaddamarwar, Ministan Wutar Lantarki, Ayyuka da Gidaje, Babatunde Raji Fashola, ya lura da cewa matakin da rukunin kamfanin Dangote ya yi ya nuna jajircewar shi mai kishin cigaban kasa ne.
Discussion about this post