Wasu hasalallu a garin Shinkafi cikin Jihar Zamfara, sun tashi da tarzomar nuna bacin ran ci gaba da matsalolin rashin tsaro a Karamar Hukumar su.
A ranar Asabar ce su ka fito kan titi, inda bayan tare hanya kuma su ka dunguma su ka kai hare-hare a Fadar Sarkin Shinkafi da wasu gidajen manyan gwamnatin jihar.
Sun kai hari fadar Sarki Muhammadu Makwashe, Sarkin Shinkafi, sannan kuma su ka sake kai hari a gidajen wasu manyan ‘yan siyasar da ke da mukamai a karkashin gwamnatin jihar Zamfara.
Wadanda aka kai hare-haren gidajen su dai kamar yadda PREMIUM TIMES ta gano, su na cikin kwamitin wadanda gwamnati ta kafa domin sasantawa da masu garkuwa da mutane da sauran hare-haren masu kwasar masu dukiyoyi.
Yayin da jihar Zamfara ta tashi haikan ta na kokarin yin zaman sulhu da ’yan bindiga, jama’a da dama a kasar nan sun nuna rashin gamsuwa da wannan tsari.
Sannan kuma zaman sulhun da ake yi bai hana mahara ci gaba da yin garkuwa da satar abinci da dabbobin jama’a da su ke yi ba.
Masu zanga-zanga sun lalata fadar sarki, sannan kuma su ka yi kira a soke yarjejeniya da zaman sulhun da ake yi da masu garkuwa.
Sannan kuma su ka nemi a bar kowa ya mallaki makaman kare kan sa kawai shi ne mafita.
Wasu mazauna garin sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa wannan zanga-zanga ta biyo bayan da masu garkuwa su ka kama wani sanannen mutumin garin wanda kuma dan bijilante ne da su ka dade su na nema su kama.
Kama wannan mutum mai suna Sama’ila Lagga da mahara su ka yi, ya harzuka jama’a da dama.
’Yan bindiga sun shiga Shinkafi har gidan Sama’ila Lagga su ka kama shi. Hakan ya harzuka jama’a fitowa zanga-zanga.
Masu zanga-zangar dai sun hakura da lalata dukiyoyi bayan da su ka samu labarin cewa mahara sun jefar da shi a gangaren wata fadama, inda jami’an tsaro su ka tsinto shi, su ka garzaya da shi asibiti. Haka dai wata majiya a garin ta tabbatar wa PREMIUM TIMES.
Sai dai kuma kakakin jami’an tsaro na Zamfara, Mohammed Shehu, ya bayyana cewa wasu marasa kishi ne su ka dauki nauyin zanga-zangar.
Ya ce kuma an kama mutum 18 da su ka gudanar da zanga-zangar, wasu har da makamai a hannun su.
Sai ya kara da cewa sace Lagga ke da wuya sai tubabbun ’yan bindiga da ‘yan sanda su ka bi sayu su ka ceto shi.
Ya ce tuni har an maida shi gida cikin iyalan sa.