Tsohon Sanata Shehu Sani ya bayyana wadannan ‘shikashikai’ 10 da ya ce duk mai sha’awar shiga siyasa sai sun hau kan sa, ko ya na so, ko ba ya so.
Shehu Sani dai ya fadi zabe karo na biyu a 2019. Ya buga wadannan ‘shikashikai’ 10 a shafin sana WhatsAPP.
1 – Kafin ka shiga siyasa, ka tabbatar ka na da isassun kudaden da za ka ragargaje su ga shugabannin jam’iyya kafin su ba ka tikitin tsayawa takara. Kuma ko ka kashe masu kudaden, ba fa lallai ne su zabe ka ba.
2 – Ka tabbatar idan ka shiga siyasa duk wanda ya kira wayar ka sai ka amsa. Kuma duk wanda ya gayyace ka taro, to sai ka halarta.
3 – Ka shirya ko da yaushe karbar ’yan jagaliya da ’yan daba a gidan ka da ofis-ofis din ka. Kuma duk inda ka shiga, tilas fa sai ka yi juriya da hakurin rashin mutuncin su da sauran munanan dabi’un su.
4 – Ko da yaushe ba ka da isasshen lokacin kan ka da na iyalin ka. Saboda kullum a cikin halartar taro ka ke. Ko kuma wasu lokutan kai da kan ka za ka rika fagamniyar gudun jama’a.
5 – Ka yi shirin juriyar a ci maka mutunci, sharri da yarfe da bata-suna. Za a rika yin kamfen din tozarta ka, ta hanyar biyan sojojin-baka su na shiga radiyo da talbijin da soshiyal midiya su na keta maka rigar mutunci.
6 – Abokan adawar siyasar ka za su bazama zakule-zakulen duk wani tarihin ka na baya. Idan ma akwai wani guntun kashin da ya taba binnewa a baya, ko wanda iyayen ka su ka binne, to sai an fito da shi. Idan kuma babu, to za a kirkiro wani kashin mai mummunan doyi a ce wa jama’a ai kai ko iyayen ka ne su ka kantara shi a baya, ku ka binne. Sharri, kage, tuggu, yarfen abin da ka yi da wanda ba ka yi ba, duk sai an rika yi maka. Hatta rigimar ka da iyali ko wani ciwo da ka taba yi, ba za su bari ba, sai sun fallasa.
7 – Ka shirya sosai saboda wadanda ka ke tunanin su ne aminan ka a siyasa, za su ci amanar ka, za su yi maka yankan-baya. Wadanda ka tsamo daga dagwalon wahala da kuncin rayuwa, za su yi kokarin dulmiyar da kai a cikin ruwan dagwalon da ka tsamo su. Ka na ji ka na gani za su sake ka su kama abokin adawar ka. Wannan abu ne mai sauki a wurin su, tamkar tubewa ko cire riga.
8 – Ka yi shirin ciwo bashi domin ka biya bukatun masu tafiyar maka da ragamar siyasa. Ka shirya sayar da kadarorin ka domin ka biya masu bukatun su.
9 – Ka shirya ji da ganin yadda wanda zai zo da rana ya yi maka rantsuwar ya na tare da kai, amma idan dare ya yi, sai a same shi gidan abokin adawar ka su na tare. Ka shirya sauraren abin da za a zo a fada maka, ko da kuwa karairayi ne.
10 – Ka shirya takura wa rayuwar ka da kan ka, ta hanyar tsananta wa jikin ka, wahalar da kai, takura wa juciya, shiga cajin kwakwarwa fiye da yadda ya kamata ka kasance a rayuwa. Ka yi shirin sauraren kulle-kullen da wasu ke yi a kan ka a kowace rana. Za ka sha jin irin labaran yunkurin ganin bayan ka da ganin bayan iyalan ka da wasu ke yi a kullum.
Siyasa ai kurde ce, wato muguwar hanya – ko malam ya bi ki sai ya yi goho.
DUK WANI DAN SIYASAR DA KA GANI, TO A CIKIN WANNAN HALIN YA KE TAFIYAR DA RAYUWAR SA.