A ranar Asabar, 2 ga Janairun 2021, Sojojin Saman Najeriya karkashin jagorancin Babban Hafsan Sojin Saman, Sadiq Abubakar da kansa suka dira ilahiran dazukan dake kewaye da titin Abuja-Kaduna domin yin atisayi da sojojin saman.
Sadiq ya ce sun yi wannan atisayi ne domin gargadin mahara cewa lokacin gamawa da su yayi yanzu, za a bisu har inda suke a fatattakia su.
” Mun samu manyan jirage yanzu, muna atisayi ne domin nuna wa mahara cewa kashin su ya bushe, za mu bisu har inda suke da sabbin jiragen mu mu dirkake su.
” Wannan atisayi zai kara wa sojojin mu kwazo da zamman tunkarar mahara a duk inda suke kuma munyi masa take da ‘Taimako Ya zo.
A karshe ya yabawa shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan maida hankali da yayi wajen ganin an kawo karshen ta’addanci a kasar nan.