KORONA: Talauci ya fi kisa fiye da duk wata cuta a Najeriya – Abba Pantami

0

Shugaban kungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani “Arewa Media Writers” na kasa Abba Sani Pantami, ya bayyana talauci ya fi saurin kisa fiye da duk wata cuta a Nijeriya.

Kungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani “Arewa Media Writers, kungiya ce da wasu marubuta suka kafa domin haɗa kai marubutan a yankin Arewa.

A zantawa da yayi da manema Labarai a garin Gombe ranar Alhamis, shugaban kungiyar Pantami, ya shawarci gwamnatin tarayya cewa a kokarin ta na siyo rigakafi na biliyoyin naira don shawo kan matsalar cutar Korona, to kamata yayi ta samar da hanyoyin da zata kawar da talaucin da ya addabi al’ummar kasar, tare da maida hankali wajen kawo karshen matsalar rashin tsaro da ya addabi kasar nan musamman yankin Arewa.

Ya kara da cewa; “Akwai bukatar daukan matakin gaggawa a bangaren lafiya, amma matsalar yunwa, da rashin tsaro sun fi illata al’umma musamman talakawa wanda sune suka fi kowa yawa inda dubunnan al’umma ke mutuwa duk wata ta sanadiyyar matsananciyar yunwa, ta’addanci, da wasu cututtuka masu kama da yunwa”.

“Baza’a taba hada cutar Korona da wadanda suke mutuwa ta sanadiyyar yunwa, ko ta’addancin da ake yi a kasar nan ba, mutum basu wuce 20 dake mutuwa a dalilin Korona a cikin sati daya, amma akan rasa daruruwan mutane ta sanadiyyar yunwa da kuma ta’addanci.”

“Gwamnatin kasar ta fi maida hankali wajen kawo karshen cutar Korona saboda masu kuɗi cutar take taɓawa, madadin sauran cututtukan da suke ta kashe talakawan ƙasar.”

“Ya kamata gwamnatin ƙasa ta kara kokari akan kokarin da take yi, wajan kawo karshen cutar yunwa da ta addabi al’ummar kasar nan, da kuma uwa uba rashin tsaro da ya addabi mutane musamman ma yankin mu wato yankin Arewa kamar yadda ta zake wajen gani an gama da Korona.”

Share.

game da Author