Shekaru 10 a jere Najeriya kashi 2% bisa 100% kadai na alkamar da ake ci ta ke iya nomawa

0

Shekaru 10 kenan a jere, duk da kokarin da ake cewa ana yi na bunkasa harkokin noma a cikin Najeriya, har yau kashi 98% bisa 100% na alkamar da ake amfani da ita cikin gida, shigo da ita ake yi daga kasashen waje.

Wannan ya na nufin kenan tsawon shekaru 10 a jere, Najeriya ba ta iya samar da fiye da kashi 2% bisa 100% na yawan alkamar da ake bukata a kasar nan, a duk shekara.

Wannan kididdiga da bin-diddigi ya fito ne da Hukumar Bunkasa Noma a Afrika ta Amurka, da aka fi sani da USDA, wadda binciken da ta gudanar tsakanin 2010 zuwa 2020 ya tabbatar da haka.

Binciken ya tabbatar da cewa yayin da ake kara bukatar amfani da alkama sosai a kasar nan, maimakon Najeriya ta maida hankali wajen noman alkama, sai ta buge wajen maida hankali ana shigo da ita daga kasashen waje.

Binciken ya kara tabbatar da cewa akalla duk shekara idan Najeriya ta yi namijin kokari, to alkamar da ta ke nomawa ba ta wuce kashi 2.6% bisa 100% din wadda ake bukata a kasar nan. Sauran duk daga waje ake shigo da ita.

Wannan karancin noman ta a cikin Najeriya ya nuna dalilin da ya sa yawancin abincin da ake hadawa da alkama a cikin kasar nan ya ke yawan tashin farashi a kai a kai, ciki har da biredi.

Bayanan kididdigar alkaluma ta nuna cewa alkamar da aka noma cikin 2018 a Najeriya ba ta wuce ton 60 kacal ba, haka cikin 2019 da 2020, amma kuma adadin yawan alkamar da aka ci a cikin wadannan shekarun ta kai ton 4760, ton 4900 da kuma ton 4319.

Binciken ya nuna rabon da a ma noma alkama mai yawan ton 100 a Najeriya, tun cikin 2010 da kuma 2012.

Yayin da ake ci gaba da samun karancin noman alkama a Najeriya, a lokaci guda kuma ana ci gaba da samun karuwar masu bukatar alkamar a cikin kasar.

Kididdiga ta nuna an ci tan 3582 cikin 2010, ton 4900 cikin 2019. Cikin 2020 ne ma aka samu dan ragin maciya alkama a kasar nan, aka yi amfani da tan 4700.

“Wannan babban abin kunya ne ga Najeriya, a kamar wannan kasa wai ba ta iya noma wadatacciyar alkamar da za ta wadace mu. Ga mu da kasar noma da duk wani abin da ake bukata domin bunkasa harkokin noma alkama, duk mu na da shi a kasar nan.” Inji Jonathan Oloniyo, wani masani fasaha da kimiyyar hada abinci, wanda ya mallaki wani gidan biredi a Abuja.

“Kai ta ma taba ganin kasar da ta zama kasaitacciya a fannin noma ba tare da ta yi amfani da kimiyya da fasaha ba? Ai ba zai taba yiwuwa a samu ba.” Inji shi.

Alkama dai idan an noma ta, a yawancin kasashe nika ta ake ana maida ta gari. Ita ce ake yin filawa a ita, daga nan kuma a rika maida ta nau’o’in abinci iri daban-daban, kamar biredi, indomi, taliya, biskit, cincin da sauran su.

Masana nagartar abinci sun ce alkama na da sinadaran gina jiki sosai, sabanin wasu nau’o’in kayan abinci masu yawa.

A Najeriya, an fi yin noman alkama a jihohin Barno, Bauchi, Yobe, Kano, Jigawa da Zamfara.

Cikin 2020 a lokacin dokar kulle mutane gida saboda korona, farashin biredi ya tashi da kashi 14 bisa 100, inda a Abuja wanda sai da ya kai har naira 400 daga tsohon farashin sa.

Share.

game da Author