Hukumar Rarraba wutan lantarki ta kasa ta bayyana cewa, tun bayan rasuwar tsohon shugaban kasa Shehu Shagari a 2018, aka dai na biyan kudin wutan gidan sa dake Kaduna.
Jaridar Daily Nigerian da ta ruwaito labarin a shafinta, ta ruwaito cewa kakakin kamfanin na Kaduna, Abdulaziz Abdullahi na cewa ba a biyan kuɗin wutar tun bayan rasuwar tsohon shugaban kasa Shagari.
Hukumar ta ce tana bin gidan marigayin na Kaduna bashin zunzurutun kudin wuta da aka kwankwada har naira miliyan 6.
Tsohon shugaban Kasa Shagari ya ya rasu yana da shekara 93.
Kakain hukumar ya kara da cewa an ba wannan gida tsawon lokaci su biya ta hanyar yi musu jinkiri da tunatar da su amma basu ce komai ba.
Daily Nigerian ruwaito cewa wani jami’in gwamnatin Sokoto wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce babu adalci idan aka ɗaurawa gwamnati laifi kan yanke wutar da aka yi wa tsohon shugaban kasa, marigari Shagari.
Sai dai kuma masu fashin baki ta tambaya cewa ko wanene hakkin kula da tsohon shugaban kasan ya rataya akan su?
Wasu na ikirarin gwamnatin tarayya ce ke kula da tsoffin shugabannin kasa da bai kamata ta bari ayi masa irin wannan cin fuska ba, wasu kuma na ganin sakacin iyalansa ne da za a ce wai an gagara biyan kudin wutan gidan Shagari tun 2018.