Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta bayyana nasarar ragargaza motocin yaki bakwai na Boko Haram da aka yi ta hanyar amfani da jiragen yaki.
Kakakin Hedikwatar Tsaron ta Kasa, John Enenche ne ya bayyana haka a cikin wata danarwa da ya fitar.
Ya ce an ragargaza jerin gwanon kwamba din motocin yakin ne a lokacin da su ke kokarin karasawa garin Marte da ke jihar Barno, domin su kai wa wasu Boko Haram agajin karin mahara.
Ya ce sojojin Operation Lafiya Dole ne su ka kai farmakin kan Boko Haram din wadanda aka tabbatar cewa bangaren ’yan ta’addar ISWAP ne.
Cikin sanarwar da ya fitar ranar Lahadi, Enenche ya ce an ragargaza motocin ISWAP din har mota bakwai bayan da farko an lalata wasu bakwai.
Ya ce bakwai na farko da aka lalata, sojojin ka ne suka ragargaza wa ISWAP su, a wani gumurzun da aka yi wanda Boko Haram din ba su ji da dadi ba.
Manjo Janar Enenche a ce kwanaki biyu a jere, tsakanin ranr 15 da 16 Ga Janairu, sojojin Njaerfiya sun yi gagarimar nasarar hana ISWAP Shiga garin Marte.
Ya ce an ragargaza jerin gwanon kwamba din din motocin yakin ne a lokacin da su ke kokarin karasawa garin Marte da ke jihar Barno, domin su kai wa wasu Boko Haram agajin karin mahara.
A karshe ya ce sojojin Najeriya ba za su taba tsayawa hutuawa ba, har sun kakkabe Boko Haram da ‘yan ta’addar ISWAP a cikin kasa.