Gwamnan jihar Barno ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta fi sauran gwamnatocin baya samar da tsaro a jihar Barno da yankin Arewa Maso Gabas.
Zulum ya fadi haka yayin da yake yin jawabi a dakin taron gidan gwamnatin jihar a lokacin da kungiyar dattawan Arewa suka kai masa ziyarar jaje kan kisan manoma 43 da Boko Haram suka yi.
” Gwamnatin Buhari ta fi gwamnatocin baya tabuka abin agani a jihar a game da tsaro. Idan aka duba kafin zuwan sa, kanana hukumomi da dama suna karkashin ikon Boko Haram ne. Hatta manyan sarakunan wadannan wurare duk sun yi kaura saboda Boko Haram.
” Amma yanzu babu wata karamar hukuma da karkashin ikon Boko Haram kuma sarakunan da suka gudu duk sun dawo yanzu.
” Kananan Hukumomin Ngala, Kukawa, Bama, Askira Uba, Dikwa, Damboa duk Boko Haram sun mamaye su amma yanzu an fatattake su. Yanzu sai hare-haren kwantan bauna su ke yi da kuma afka wa mutanen da basu ji ba basu gani ba.
Haka kuma a baya, Boko Haram za su bugi kirji su afka barikin sojoji, kamar yadda suka yi a Bama da wasu wuraren amma yanzu basu iya haka saboda an karya lagon su.
Zulum ya kara da cewa mutane na da mantuwa ne saboda abInda ke faruwa yanzu yanzu shine yafi damun su, sukan manta da jiya.