Masana ilmin hada magunguna dake aikin hada maganin rigakafin cutar Korona sun ce nan da karshen 2021 kowa da kowa zai samu maganin rigakafin cutar Korona.
Malaman dake aiki da kamfanin BioNTech da Oxford ne suka fadi haka a taron tattauna hanyoyin dakile yaduwar cutar da UN ta shirya.
Zuwa yanzu kasar UK ita ce ƙasa ta farko a duniya da ta amince da maganin rigakafin korona da kamfanonin Pfizer da BioNTech suka hada.
Gwajin sahihanci da ingancin maganin da hukumar MHRA ta yi ya kai kashi 95.
Tuni wadannan kamfanonin sun fara yi wa mutane allurar rigakafin cutar da maganin da suka hada a Disemba.
kamfanin Pfizer dake kasar Amurka da Kamfanin BioNTech dake kasar Jamus suka Sanar cewa sun hada maganin rigakafin kamuwa da kwayoyin cutar korona dake da aka tabbatar da ingancin sa da akalla kashi 90 bisa 100.
Wadannan Kamfanonin sun hada wannan magani ƙasa da lokacin da ake zaton za a kammala hada shi kuma har sun yi gwajin ingancin sa a jikin mutane sama da 44,000.
Kamfanonin na sa ran cewa gwajin ingancin maganin da ake yi ba zai dauki tsawon lokaci ba domin samun izinin fara amfani da maganin.
Discussion about this post