Jam’iyyar APC ta ce nasarar da jam’iyyar ta yi a zabukan cike gurabu da aka yi ya tabbatar da farin jinin Buhari da kuma tabbatar wa ƴan adawa cewa har yanzu talakawa na tare da Buhari 100 bisa 100.
APC ta yi nasara a jihohi bakwai cikin 11 da aka gudanar da zaben cike gurbi.
Jihohin da PDP suka yi nasara sun hada da Zamfara, Bayelsa, Enugu da Koross Ribas.
APC kuma ta yi nasara a jihohin Lagos, Imo, Kogi, Plateau, Katsina, Bauchi da Borno.
Baya ga kin fitowa zabe da mutane suka yi, duk da haka sai da aka tafka magudi a wasu wuraren.
Discussion about this post