Gwamnan jihar Jigawa Mohammed Badaru, ya bayyana cewa akwai yiwuwar Jam’iyyar da ta kawo sa mulki a 2015 da 2019 ta sha kasa a 2023 muddun ba a dinke barakar da ta yagalgala jam’iyyar a jihar ba.
Badaru ya fadi haka yayin da yake rantsar da shugabannin riko na jam’iyyar a garin Dutse.
” Da ga yanzu zan sa ido akan abubuwan dake suke faruwa a jam’iyyar, duk wanda ya ke yi mana zagon kasa ko yankan baya, w zai kuka da kansa. Hakurin namu ya isa hakanan.
” Maimakon mu rika koyon yadda jam’iyyar ke gudanar da al’amuran ta a jihohin Barno da Yobe, wanda tunda aka faro siyasa basu taba samun matsala ba mum bari a jihar an samu rarrabuwan kai. Ina gaya muku idan ba a yi taka-tsantsan ba zamu fadi ragas a 2023.
Badaru yayi kurin shi babban dan kasuwa ne, ba ya bukatar siyasa bayan 2023, ” Saboda haka ku sani ni gawurtaccen dan kasuwa ne da zai iya zuwa duk kasar da nake son zuwa ba tare da na rike koda jakar hannu ba. Saboda haka kune kuke bukatar siyasa.
A karshe yayi kira ga bangaren dake adawa da gwamna Badaru su dawo a yi tafiyar tare.
Sai dai kuma tsohon shugaban jam’iyyar da basu ga maciji a tsakanin su da bangaren gwamna Badaru, Habibu Sara ya yi watsi da korafin gwamnan.
Sara ya ce dama abin da suke gudu kenan, yasa suke ta yaki da gwamnan, ” Mun san da haka, mun san da kulle-kullen da yake yi wa APC a Jigawa, Saboda shi dan kasuwa ne yayi amfani da kujerar gwamna ya azurta kan sa. Idan 2023 yayi sai ya tattara kayar sa ya koma kasuwa.
Mu kuma da ba sana’ar mu ba ce, Siyasa ce sana’ar mu, dole mu tsare ta mu kare ta mu yi mata shinge da irin su Badaru.
‘Bakin sa ya sari danyen Kashi’, APC ce zata kafa gwamnati a Jigawa a 2023.