Yayin da cutar korona ta dawo gadan-gadan, Shugaban Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA), ya bayyana cewa likitoci 20 su ka mutu a wannan makon sanadiyyar cututtuka masu alaka da korona.
Enema Amodu ya bayyana wannan tashin hankali a ranar Juma’a wurin taron manema labarai, inda ya ce wadanda su ka mutu din sun hada da jami’an lafiya da na tuntuba da wasu farfesoshi da tantagaryar likitoci.
Ya ce yawan wadanda ke mutuwar na karuwa a kullum.
“ Mu da ke aikin harkokin kula da lafiya, mun rasa abokan aikin mu da dama. Wadanda korona ta kashe a cikin mako daya kadai a fadin kasar nan, sun kai likitoci 20.” Inji shi.
Jami’an kiwon llafiya na fadawa tarkon saurin kamuwa da cutar, saboda su ne ke fara tunkarar wanda ya kamu da cutar.
Duk da cewa su kan su jami’an kula da lafiya da likitocin su kan su ana gargadin su rika amfani da rigunan kariya daga hada jiki da wanda ya kamu da korona, da yawan su ba su da sukunin samun kayan kariyar.
Idan ba a manta ba, sama da jami’an kula da lafiya 1,000 ne su ka kamu da cutar korona a Najeriya.
Hukumar Kula da Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (WHO), ta ce zuwa Yulin da ya gabata sama da jami’an kula da lafiya 10,000 ne suka kamu da cutar korona a fadin Afrika.
Sai dai zuwa yanzu ba za a ma iya tantance adadin yawan jami;an kiwon lafiyar da su ka kamu ba a Najeriya.
Amodu yay i gargadin a tashi tsaye wajen kare kai daga kamuwa, domin a yanzu da korona ta sake dawowa, ta fi ta baya karfi da saurin kassara mutane gadan-gadan.
Ya ce a yanzu jama’a ba su daukar matakan kariya da muhimmanci, kuma babu kayan kariyar a wurare da dama, kamr yadda aka rika sayarwa a watannin baya, farkon bullar cutar.
Dawowar da korona ta yi da wani sabon samfuri mueamman a Turai, ya sa Najeriya ta kakaba tsauraran ka’idoji ga fasinjojin masu shigowa daga Birtaniya da Afrika ta Kudu.
Sanadiyyar gano wata nau’in cutar korona da aka yi kwanan nan a wasu kasashe, gwamnatin Najeriya ta fito da wasu sabbin tsautsaran ka’idoji ga masu shigowa kasar nan daga Ingila da Afrika ta Kudu.
Kodinatan Kwamitin Yaki da Cutar Korona na Kasa, Sani Aliyu ne ya bayyana haka a lokacin da kwamitin sa ke wa manema labarai karin haske kan halin da ake ciki kan korona a kasar nan.
“Daga ranar Litinin 28 Ga Disamba, 2020, duk wasu fasinjoji da za su shigo kasar nan daga Birtaniya da da Afrika kai-tsaye ba tare da sun yada zango wata kasa ba, to sai sun cika Rajistar Sharuddan Tafiye-tafiye na Najeriya a intanet tukunna.
“Dole ya kasance sun cika tambayoyin da za a yi masu a shafin intanet din, kuma su yi firintin na takardar shaidar cewa ba su dauke da cutar korona.
“ Sannan kuma ya kasance takardar shaidar ta su ba ta wuce kwana biyar da yin gwaji ba”.
Ya ce za a bude wannan rajista a tashoshin jiragen sama domin fasinjojin da za su shigo daga wadannan kasashe, don a tabbatar cewa sun gabatar da kan su an yi masu gwajin cutar korona a rana ta bakwai da isowar su.
Tuni dai sama da kasashe 40 ne su ka hana jiragen sama sauka kasar su daga Birtaniya, sakamakon gano wata cutar korona wadda ta fi wadda ake fama da ita saurin fantsama da kuma saurin kama mutane.
Wasu kasashen da su ka hana saukar fasinjoji daga Birtaniya, sun hada da Indiya, Pakistan, Rasha, Jordan, Hong Kong da kasashen Turai kusan baki daya.
Su kuwa kasashen Saudiyya da Kuwait da Oman sun rufe kasashen su baki daya, ba shiga ba fita.