KORONA: Mutum 712 suka kamu ranar Juma’a, ranar Kirsimeti

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 712 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Juma’a.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –388, FCT-77, Kwara-39, Katsina-35, Bauchi-33, Filato-22, Ogun-18, Akwa Ibom-16, Delta-13, Kaduna-12, Osun-12, Yobe-11, Sokoto-10, Kebbi-8, Enugu-6, Edo-5, Ondo-3, Niger-2, Kano-1 da Oyo-1.

Yanzu mutum 82,747 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 70,239 sun warke, 1246 sun rasu.Sannan kuma zuwa yanzu mutum 11,255 ke dauke da cutar a Najeriya.

A ranar Alhamis, mutum 1041 suka kamu a Najeriya, jihohin Kaduna, Legas, Filato, Gombe da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 28,192, FCT –10,766, Oyo – 3,878, Edo –2,819, Delta –1,868, Rivers 3,328, Kano –2,134, Ogun–2,449, Kaduna –4,804, Katsina -1,570, Ondo –1,798, Borno –789, Gombe –1,248, Bauchi –945, Ebonyi –1,097, Filato – 4,459, Enugu –1,382, Abia – 983, Imo –748, Jigawa –389, Kwara –1,379, Bayelsa –519, Nasarawa –665, Osun –1004, Sokoto – 209, Niger – 409, Akwa Ibom – 429, Benue – 524, Adamawa – 355, Anambra – 307, Kebbi – 163, Zamfara – 79, Yobe – 187, Ekiti –409, Taraba- 211, Kogi – 5, da Cross Rivers – 166.

Shugaban Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA), Enema Amodu ya bayyana cewa likitoci 20 su ka mutu a wannan makon sanadiyyar cututtuka masu alaka da korona.

Amodu ya ce yawan wadanda ke mutuwar na karuwa a kullum.

“ Mu da ke aikin harkokin kula da lafiya, mun rasa abokan aikin mu da dama. Wadanda korona ta kashe a cikin mako daya kadai a fadin kasar nan, sun kai likitoci 20.” Inji shi.

Jami’an kiwon lafiya na fadawa tarkon saurin kamuwa da cutar, saboda su ne ke fara tunkarar wanda ya kamu da cutar.

Duk da cewa su kan su jami’an kula da lafiya da likitocin su kan su ana gargadin su rika amfani da rigunan kariya daga hada jiki da wanda ya kamu da korona, da yawan su ba su da sukunin samun kayan kariyar.

Share.

game da Author