Tsohon mataimakin shugaban Kasa Atuku Abubakar ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka dokar ta baci a jihohin da rashin tsaro yayi tsanani.
Atiku ya ce lallai fa lokaci yayi da za a dai na boye-boye da maida komai siyasa, a fadi gaskiya komai dacin ta, maganan tsaro fa ya yi taɓarɓarewar da yana neman yafi karfin gwamnati.
” Buhari ya saka dokar ta baci a jihohin da ake fama da tsananin rashin tsaro a kasar nan tunda wuri. Dokar kasa ta tsara yadda ake yi. Ba zai shafi tsarin kujerun siyasa dake jihohin ba, amma yanzu kama hakan shine mafita, domin a iya tunkaran ta’addanci gaba-da-gaba.
” Ko wa dai ya sani kuma ya gani cewa dabarun da ake amfani da su wajen kawo karshen ta’addanci a tsawon shekaru biyar din da suka wuce bai haifar da da mai ido ba. Ga shi kwatsam kuma an shiga makarantar kwana an kwashe dalibai, wannan tashin hankali da me yayi kama.
Atiku ya bada shawaran a dakatar da makarantun kwana a wadannan jihohi, a koma ta jeka ka dawo har zuwa lokacin da za a samu saukin ta’addanci a wadannan jihohi.
Bayan haka, Atiku ya ce lallai jami’an tsaron kasa su tabbata sun dawo wa kowani uba da dansa sannan su kamo wadannan ƴan ta’adda da suka kaikata wannan mummunan abu.
Idan ba a manta ba mahara sun yi wa Buhari barka da zuwa Jihar Katsina da yin garkuwa da yaran makarantan sakandaren Kankara.
Mahara sun daka warwason yaran makarantan kwana dake kankara ranar juma’a a harin da suka kai makarantar cikin dare.
Shugaba Buhari ya yi tir da wannan hari inda ya umarci jami’ an tsaro su gaggauta zakulo wadanda suka kai wannan hari sannan su ceto yaran da suka yi garkuwa da.