HIMMA DAI MATA MANOMA: Manoman Najeriya na bukatar na’urori masu saukin sarrafawa -Zainab Isah

0

Zainab Isah mai shekaru 52 da ‘ya’ya bakwai, ta rike harkar noma gadan-gadan a Zamfara.

Ta bayyana wa wakilin mu cewa ta na noma wake, dawa, sai kiwon kifi da kiwon kaji, waken soya da masara da shinkafa.

“Tashin farko ni zan iya cewa a gona aka haife ni. Don haka ni noma tamkar gado na yi a wurin mahaifi na. A haka na rika hada harkar noma da karatu.”

Da aka tambayi Zainab yadda ta ke samun gonakin da ta ke nomawa, sai ta ce, “Ai ka san mu nan Arewa gonaki ba matsala ba ne. Za ka iya saye da kudin ka, ko ka ci gado daga iyayen ka, ko kuma ka karbi aro ko gingina.”

“Ina da nawa gonakin, inda da wadda na ci gado kuma ina da wadanda na ke jingina.”

“Gonar da na saya da kudi na, ta kai fadin hekta daya, kuma ita ce babba a cikin su. Akwai wadanda na ke jingina, amma a cikin gurup na kungiyar manoma mata.

“Kuma ba ni da matsala da irin shuka, saboda duk na zamani ke amfani da su.

Wasu irin a gona ta na ke adana su, ko noma su. Kuma saboda gurbacewar yanayi, ana karfafa mana guiwa mu rika noma amfanin gonar da za mu rika debewa da wuri, saboda gudun ambaliya ko wani ibtila’i.”

Zainab ta ce babbar matsalar ta shi ne rashin kayan noma na zamani.

“Mu kananan manoma musamman na nan Arewa, mu na da bukatar kayan noma na zamani. Saboda komai ci-da-karfi mu ke yi.

“Ni ina da shunuj da ke yi min huda. To amma ai akwai sauran aikace-aikacen gona masu bukatar amfani da na’ura kamar motocin noma da sauran injina. Sai da su za mu iya noma wadataccen kayan abincin da zai wadaci kasa.” Inji Zainab.

Zainab ta ce ta gaji noma wajen mahaifin ta. Shi ya koya mata a gonar sa. Ita ma za ta so yaran ta su rika taya ta domin ta sa su a hanya.

Ta ce ita noman ta na kasuwanci ne, sayarwa ta ke yi. Kuma ta na kaiwa a kasuwannin kauye, sannan gwamnati na saye a hannun ta.

Ta ce ta na da alaka da Kungiyar Kananan Manoma Mata ta Kasa.

“Da a ce zan samu kayan bunkasa noma na zamani, to da zan fi haka sosai, kuma zan fi maida himma wajen bayar da gudummawar noma abincin da zai kara bunkasa da wadatar da kasar nan.”

Share.

game da Author