Huhhura hanci, nuna Isa da murza gashin baki ba zai ba mu Shugabancin Najeriya ba – Inji Anyim

0

Tsohon Shugaban majalisar Dattawa, Pius Anyim Pius ya bayyana wasu matakai da iadan ‘yan kabilar Igbo suka za su iya kaiwa ga samun zama shugaban kasa a Najeriya.

Anyim ya fadi a awani taron ‘yan Kabilar Igbo da aka yi a jihar Abia cewa, abu biyu da Inyamirai za su yi su iya kaiwa ga yin nasarar darewa shugabancin Najeriya a 2023 shine fa idan suka kwantar da hankalin su su ka daina ganin su ne shafaffu da mai a kasar nan suna raina wasu.

” Muna raina abokan zaman mu muna nuna su ba kowan-kowa bane, mune muka isa, mu ci musu mutunci muna musu izgilanci, yin haka ba zai kai mu ga samun shugabancin Najeriya ba. Dole mu kwantar da hankalin mu mu jawo kowa a jika, mu lallashi abokan zaman su idan muna son wata rana mu dare kujeran.

Anyim ya kara da cewa yanzu dai ya nuna kakara cewa yankin na bukatar zama shugaban kasa amma kuma samun haka ba zai yiwu ba ” idan muka ce za mu rika ganin mu shafaffu da mai ne, muna fankama, muna nuna ‘yan wasu yankin ba su isa ba. Mu ne dai za mu kwantar da hankalin mu mu hada kan mu sannan mu jawo sauran ‘yan uwan mu da muke zama tare mu nuna musu soyayya da yarda, idan ba haka ba sai dai fa ga an yi mun zama ‘yan kallo.

Ya ce 2023 gaba dayan su burin su shine a samu hadin kan Inyamirai kuma su yi nasarar darewa kujerar shugabancin Najeriya.

Share.

game da Author