Majalisar Dattawa ta amince da Kasafin 2021, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar, sannan kuma ta kara yawan sa daga naira tirliyan 13.08 zuwa naira tiriliyan 13.6.
Cancak dai a yanzu kasafin na 20121 ya koma naira 13,588,027,886,107.
Sun yi karin ne a bangaren manyan ayyuka, wanda a yanzu ya tashi daga naira tiriliyan 3.6 zuwa naira tiriliyan 4.1.
An amince da Kasafin ne bayan gabatar da shi da Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Kasafin Kudi, Barau Jibrin ya yi, a ranar Litinin.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga yadda ita ma Majalisar Tarayya ta amince da kasafin kudin.
A karkashin kasafin dai za a kashe naira 3,324,380,000,000 wajen biyan basussuka cikin shekarar 2021.
Sannan kuma za a kashe nai 5,641,970,060,680 wajen ayyuka nay au da kullum. A manyan ayyuka kuma za a kashe naira 4,125,149,354,222. Yayin da za a ciwo bashi na naira 5,196,007,992,292.
Da ya ke bayani, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya gode wa majalisar tare da jinjinawa, sannan kuma ya yi kira ga jama’a su sa-ido wajen ganin an gudanar da ayyukan da aka tsara za a yi da kudaden.
Dangane da gibin naira tiriliyan biyar kuwa, tun da farko a cikin Oktoba 2020 Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa za a samu gibin naira tiriliyan 4.28 a Kasafin 2021.
Da ya ke bayanin yadda za a cike gibin, Buhari ya shaida wa gamayyar majalisin Dattawa da Mambobin Tarayya cewa bashi za a ciwo domin a yi wa al’umma ayyukan raya kasa, saboda kudaden shigar da Najeriya ta yi hasashen tarawa, ko kadan ba za su isa a yi manyan ayyukan da su ka kamata a yi da su ba.
Buhari ya ce cikin 2021 za a kashe naira bilyan 501.19 wajen biyan kudaden fanshon tsoffin ma’aikata.
Ya ce za a kashe naira tiriliyan 3.124 wajen biyan basussukan da su ka yi wa Najeriya katutu.
Hukumar Bunkasa Yankin Neja-Delta (NDDC) za ta samu naira bilyan 63.51. Hukumar Farfado da Yankin Arewa maso Gabas za ta samu naira bilyan 29.70, sai Hukumar Bunkasa Ilmi a Matakin Farko (UBE) ta za samu naira bilyan 70.
Za a bai wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) naira bilyan 40, sai Majalisun Dattawa da ta Tarayya naira bilyan 120.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana yadda aka cimma shata hasashen kashe naira tiriliyan 13.08 a Kasafin Najeriya na 2021.
Wannan ne karo na shida da Buhari ya gabatar da kashe kasafin shekara-shekara tun bayan hawan sa mulki a 2015.
Ya gabatar da na 2016, 2017, 2018, 2019 da kuma na 2020 a shekarun baya a jere.
Kasafin wanda aka rada wa suna, “Kasafin Fardado Da Tattalin Arziki”, Buhari ya ce an tsara shi a matsayin sharar-hanyar kudirin gwamnatin sa na bunkasa tattalin arzikin Najeriya a karkashin Shirin NDP 2021 – 2025.
Ya ce an kintacen farashin gangar danyen man fetur a kan dala 40, wanda akan wannan ma’auni ne aka yi kasafin dungurugum.
Sannan ya kara da cewa an sake auna ma’aunin a kan kowace dala daya daidai da naira 376.
Ya ce an yi kasafin a bisa hasashen za a rika hako danyen mai ganga milyan 1.86 a kowace rana.
Discussion about this post