Da Sanata Uba Sani zai zama gwamnan Kaduna da.., Daga Moh’d Ibn Mohammed

0

Jihar Kaduna ta samu canjin da bata taba samun irin sa ba a tun bayan kirkiro ta a Kasa Najeriya.

Gwamnatoci da dama sun zo sun wuce, kowa munga irin kamun ludayin sa, yayi watangaririyarsa ya wuce. Da yawa sun haka ramuka ne basu cike su, wasu kuma sun bada huda ne basu saka auduga ko kyalle sun goge fuskar da kyau ba.

Tun bayan dawowar dimokradiyya a kasar nan, wato a 1999, jihar Kaduna ta yi samfurin gwamnoni dai dai har biyar.

Ahmed Makarfi, Namadi Sambo, Patrick Yakowa, Ramalan Yero sai gogan aiki, in baka yi bani wuri, guduma mai fasa taro, Mal Nasir El-Rufai.

Gwamna Nasir El-Rufai, ba tun yanzu ba ya nuna jarumtar sa da son aiki ga talakawa da ci gaban al’umma ba, tun yana ministan babban birnin Tarayya, Abuja, mazauna sun shaida yadda ya maida garin Abuja, babban birni.

El-Rufai ya samu wannan lambar yabo a duniya ba kasa Najeriya ba kadai.

Sai dai kuma duk inda kaga miya ta yi jajawur tana ta bada kamshi ta hana makwabta sakat, ba manjar bace kawai, tumatirin da aka hada miyar gangariya ce.

Hakan ya nuna karara, a mulkin gwamnatin Kaduna, wadanda ke kewaye da gwamna El-Rufai ba ragwage bane, suma ina ka fito aiki ne, ina zaka aiki.

Daya daga cikin muhimman nadin da gwamna El-Rufai yayi a lokacin da ya dare kujerar gwamnan jihar Kaduna, shine nadin Mal Uba Sani, jarumi abokin tafiya, Amini mai amana, aboki mai tawali’u, gogan aiki jagoran yakin siyasar talakawan Kaduna.

Tun daga wannan rana Mal Uba Sani bai kwanta barci ba da idanu biyu a rufe, a kullum ya kwanta, kwayar idon sa daya a bude take washar yana lissafin me aka manta, me ne ne ba a yi ba don talakawar Kaduna, da kuma wace shawara zai ba gwamna a ci gaba da samun nasara da cigaba a jihar Kaduna.

Hannayen sa a bude suke, yana ciyarwa yana badawa yana tallafawa yana kokarin kai dauki.

Wannan halaye na malam Uba Sani kadan ne daga cikin halayen kirkin sa da ba za su kirgu ba.

Idan da Uba zai zama gwamnan Kaduna, da shi kenan ‘yan Kaduna su kam shar, domin inda Malam ya tsaya nan Malam zai ci gaba, shi ya sa tun farko abin ya hadu ga Mal Nasir da Mal Uba.

Yanzu dai Mal Uba Sani ya zama sanata, yana can majalisar dattawa ya na kwararo wa mutanen Kaduna ta Tsakiya romon dimokradiyya babu kakkautawa.

Mu dai fatar mu shine, Allah ya yayi mana canji da wani Malam idan wa’adin wannan Malam din ya cika, Kaduna ta fi birnin Alkahira.

Share.

game da Author