Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1041 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Alhamis.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –316, FCT-210, Kaduna-83, Filato-70, Gombe-56, Oyo-56, Katsina-47, Nasarawa-35, Kano-33, Ogun-21, Rivers-17, Niger-14, Imo-14, Delta-12, Kwara-12, Edo-12, Benue-9, Anambra-8, Taraba-4, Ekiti-4, Ebonyi-6, Bayelsa-1 da Sokoto-1.
Yanzu mutum 81,963 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 69,651 sun warke, 1242 sun rasu.
A ranar Laraba, mutum 1,133 suka kamu a Najeriya, jihohin Kaduna, Legas, Filato, Katsina, Sokoto da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 27,804, FCT –10,689, Oyo – 3,877, Edo –2,814, Delta –1,855, Rivers 3,328, Kano –2,133, Ogun–2,431, Kaduna –4,792, Katsina -1,531, Ondo –1,799, Borno –789, Gombe –1,248, Bauchi –912, Ebonyi –1,097, Filato – 4,437, Enugu –1,376, Abia – 983, Imo –748, Jigawa –389, Kwara –1,340, Bayelsa –519, Nasarawa –665, Osun –992, Sokoto – 280, Niger – 407 , Akwa Ibom – 413, Benue – 524, Adamawa – 355, Anambra – 307, Kebbi – 155, Zamfara – 79, Yobe – 176, Ekiti –409, Taraba- 211, Kogi – 5, da Cross Rivers – 94.
Ganin yadda korona ta sake dawowa gadan-gadan a Najeriya, gwamnatin tarayya ta bijiro da sabbin dokokin kokarin dakile fantsamar ta, duk kuwa da cewa a yanzu ne ma cutar ta fi yaduwa da saurin kama mutane.
A kan haka ne gwamnatin tarayya ta hannun Kwamitin Yaki da Cutar Korona, ya umarci jihohi su bijiro da dokokin hana taruka a jidajen giya da sauran wuraren sharholiya da tarukan nishadin hululu, inda ake haduwa a cinkushe.
Haka nan kuma an hana shiga gidajen cin abinci a zauna a ci a yi tatil, sai dai a shiga a saya, a dauka a tafi gida a ci.
Tarukan bukukuwa ma an gindaya ka’idar ceewa kada a rika wuce mutum 50.
Dama kuma wurare irin su sitadiyan har yanzu ba a bari masu kallo na shiga ba.
Sai dai kuma har yanzu tun da aka fara korona cikin Janairu har yau, ba a hana jama’a da manyan ‘yan siyasa taruwa a wurin kamfen ba.
Sannan wannan doka da aka bijiro da ita, ba ta ce a rufe masallatai da coci ba, amma kuma NCDC ta ce idan abin ya kara muni, to za a iya saka dokar kulle jama’a a gidajen su.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya umarci jihohi su dauki nauyin aikin kariya da kakaba dokokin da za su rage fantsamar cutar a cikin fadin kasar nan.
Kwamitin PTF ya sanar cewa za a dauki matakan hana yaduwar cutar gadan-gadan har tsawon nan da makonni biyar masu zuwa.
“Saboda haka an kulle dukkan gidajen giya, gidajen rawa da sauran wuraren tarurrukan nishadin hululu.
“Haka gidajen abinci du kana sanar da kulle su da gaggawa, amma banda gidajen abincin da ke dafa abinci a cikin otal-otal.
Sannan kuma an umarci ma’aikata daga mataki na 01 zuwa na 12 duk su zauna a gida. Wuraren ibada ma an ce ba a son sama da mutum 50.
Discussion about this post