An bada sanarwar rasuwar Musa Kwankwaso a safiyar Juma’a. Musa shi ne mahaifin Rabiu Kwankwaso, tsohon Gwamnan Jihar Kano, kuma tsohon Ministan Tsaro.
Kafin rasuwar sa shi ne Hakimin Kwankwaso, kuma Makaman Karaye. Ya rasu ya na da shekaru 93 a duniya.
Kwankwaso shi ne dagacin Kwankwaso, amma daga baya aka maida shi Hakimin Madobi, kuma Majidadin Sarkin Kano Ado Bayero.
Baya-bayan nan aka nada shi Makaman Karaye, wanda Sarkin Karaye Ibrahim Abubakar II ya nada shi. Sarkin Karaye na daya daga cikin sarakunan da Gwamna Ganduje na Kano ya nada.
Wata sanarwa da magatakardar Rabiu Kwankwaso, Muhammad Ali ya fitar a safiyar Juma’a, na dauke da bayanin cewa za a yi jana’idar mahaifin tsohon gwamnan Kano a ranar Juma’a karfe 3 na rana, a gidan Rabi’u Kwankwaso da ke Miller Road, Bompai, Kano.
Sanarwar ta ce mahaifin Rabiu Kwankwaso ya bar ‘ya’ya 19, matan aure biyu da jikoki da dama.
Sanarwar ta ci gaba da cewa saboda annobar korona da ake fama da ita, an dauke wa mutane na nesa zuwa ta’aziyya da jana’ida, musamman mutane daga garuruwa daban-daban.