Ministan Yada Labarai Lai Mohammed, ya bayyana ce an yi rugu-rugu da Boko Haram, ba su da wani karfi, sai dai harin ki-fadi kadai da su ke kaiwa na sari ka noke, akan farar hula.
Lai ya ce tuni sojojin Najeriya su ka yi wa Boko Haram laga-laga, sai su ka koma kai harin tsoro, su kar farmaki su tsere.
Lai ya yi wannan ikirari a taron sa da mawallafa jaridun kasar nan a Lagos, wato Kungiyar NPAN.
“Babu wata kasa duk irin karfin ta da za a ce ta fi karfin a kai mata harin ta’addanci. An kai harin 11 Ga Satumba a Amurka, kasar da ta fi kowace kasa karfin tsaro a duniya.
“A yanzu Boko Haram na samun kuzari ne ta hanyar farfagandar karairayin da ta ke watsawa, har jaridu na bugawa. Dubi dai yadda su ka watsa bidiyon daukar nauyin kisan mutane a Zabarmari, don kawai su cusa tsoro a zukatan jama’a.
“Saboda haka mu na kara kira ga jama’a su kara kaimi wajen labarta wa jami’an tsaro inda su ka san Boko Haram da sauran mahara sun yi mafaka, domin su magance ta’addanci..
Lai ya ce kisan da aka yi wa manoma 43 ba alama ba ce mai nuna gazawar sojojin Najeriya.
Ya ce sojojin kasar nan sun yi gagarimar nasara a kan Boko Haram.
“Sojoji sun yi wa Boko Haram rugu-rugu. To shi wanda aka yi galaba a kan sa, ba ya saurin mika wuya sai ya yi borin-kunya. Shi ya sa Boko Haram ke lababawa cikin jama’a su na kai hare-hare, don kawai a ga kamar su na da karfi, har su rika tsorata mutane. Amma duk ki-fadi ne kawai su ke yi.”
Lai ya ce masu kiran Buhari ya sauka, ba kishin kasar nan su ke yi ba, siyasa ce kawai su ka mayar da matsalar tsaron da ake fama da ita.