ZABEN DASS: Za a goge raini tsakanin Gwamna Bala da Yakubu Dogara

0

Ranar Asabar 5 ga watan Disamba, ne za a gudanar da zaben cike gurbi na mazabar Dass.

Wannan zabe an yi masa suna da zaben goge raini tsakanin gwamnan jihar Bala Mohammed da tsohon kakakin majalisar tarayya, Yakubu Dogara.

Karamar hukumar Dass na daga cikin yankin da Dogara ke da karfin iko.

Idan ba a manta ba mahara suka kashe dan majalisar dake wakiltar Dass a wani farmaki da suka kai masa wanda yasa INEC zata yi zaben cike gurbi a mazabar Dass din.

A kamfen din da Dogara yayi a karamar hukumar, ya bayyana cewa gwamnan Kano jihar Bala ya yaudari mutanen jihar Bauchi ne har ya zama gwamna ashe likimo yaya musu sai yanzu yake nuna musu halinsa karara.

A duk inda ya samu dama gwamna Bala sai ya caccaki Dogara, ya sha alwashin sai ya kunya tashi a wannan zabe.

Gwamna Bala yayi kurin cewa babu wani gudunmawa da Dogara ya bashi ko kuma yayi masa a lokacin zaben da yayi nasaran kada gwamnan Mohammed na APC.

Shi ko Dogara ya ce zai tabbata dan takarar APC ne ya lashe wannan kujera domin tare da wasu gaggan ƴan APC sun dira filin wasa na Dass domin yin Kamfen din Karshe kafin zaben gobe.

Cikin kurin da gwamna Bala yayi, ya ce shi ba gwamnan rabawa talakawa babura da kekunan adaidaita sahu ba ne wato keke NAPEP, wanda an shaidi Dogara da kokarin yi wa matasa da magidanta irin wannan tallafi domin su dogara da kansu, Bala ya ce na shi salon shine ya kawo cigaba a jiha.

Za a gudanar da zaben cike gurbin ne ranar Asabar 5 ga Disamba.

Share.

game da Author