KORONA: Mutum 343 sun kamu ranar Alhamis, Yanzu mutum 68,303 suka kamu a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 343 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Alhamis.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –106, FCT-123, Kaduna-72, Nasarawa-14, Rivers-5, Bauchi-4, Imo-4, Ogun-4, Ekiti-3, Edo-2, Oyo-2, Filato-2, Akwa Ibom-1 da Kano-1

Yanzu mutum 68,303 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 64,291 sun warke, 1,179 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 2,833 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 23,545, FCT –6,991, Oyo – 3,730, Edo –2,705, Delta –1,824, Rivers 3,006, Kano –1,799, Ogun –2,237, Kaduna –3,245, Katsina -1,030, Ondo –1,728, Borno –745, Gombe – 938, Bauchi –778, Ebonyi –1,055, Filato – 3,904, Enugu – 1,332, Abia – 926, Imo –681, Jigawa – 331, Kwara –1,110, Bayelsa – 454, Nasarawa – 507, Osun –947, Sokoto – 166, Niger – 298, Akwa Ibom – 340, Benue – 496, Adamawa – 261, Anambra – 282, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 100, Ekiti – 377, Taraba- 163, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.

Bayan haka masana kimiya ke kokarin hada maganin rigakafin korona kamfanin Pfizer dake kasar Amurka da Kamfanin BioNTech dake kasar Jamus sun hada maganin rigakafin kashe kwayoyin cutar korona da aka tabbatar da ingancin sa da akalla kashi 90 bisa 100.

Wadannan Kamfanoni sun hada wannan magani ƙasa da lokacin da ake zaton za a kammala hada shi kuma har sun yi gwajin ingancin sa a jikin mutane sama da 44,000.

Kamfanonin na sa ran cewa gwajin ingancin maganin da ake yi ba zai dauki tsawon lokaci ba domin samun izinin fara amfani da maganin.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ce kungiyar dake kula da ingancin magungunan da masana kimiya a fadin duniya ke kokarin hadawa.

Bisa ga ka’ida hada maganin zai dauki tsawon shekara daya da wata shida ne.

Kungiyar na sa ran samun biliyoyin ruwan maganin nan da shekara 2021 domin raba wa kasashen duniya.

Share.

game da Author