Akwai yara kanana da matasa sama da biliyan 2 da ‘Intanet’ bai kai gare su ba a duniya

0

Rahoton UNICEF ya nuna cewa yara da matasa biliyan 2.2 basu iya sarrafa Komfuta ballantana kaiwa ga iya amfani da yanar gizo wato ‘Internet’ a fadin duniya.

Hakan na nuna cewa an bar yara da matasa da dama a baya a wannan yanayi da komai ya koma ana yin shi ne a yanar gizo wato ‘Intanet’.

Sannan kuma hatta karantarwa ya koma ana yin su ne a shafukan yanar gizo.

Asusun UNICEF da ITU ne suka fitar da wannan rahoto na bincike da suka gudanar.

Bisa ga rahoton yaran makaranta masu shekaru 17 biliyan 1.3 da matasa miliyan 760 masu shekaru 14 zuwa 24 basu da ‘Intanet’ a gidajen su domin amfana da kimiyar zamani.

Matsalar rashin yanar gizo da yara da matasa ke fama da shi a duniya yafi yawa a kasashen masu tasowa.

A kasashe masu tasowa kashi 6 ne ke iya amfani da yanar gizo a gidajen su sannan a kasashen da suka ci gaba yara da matasa kashi 87 ne ke amfani da yanar gizo a gidajen su.

Kashi 25 na yara da matasa talakawa ne ke samun ‘Intanet’ a gidajen su kuma kashi 41 na ‘ya’yan masu hali ke amfani da yanar gizo a gida.

Matsalolin dake hana rashin samun yanar gizo.

Rahoton ya nuna cewa talauci, wuraren zama na daga cikin matsalolin dake hana yara da matasa samun ‘Intanet’.

Rashin samar da yanar gizo a makarantu ko a gida ya kawo cikas ga karatun yaran makaranta musamman a wannan lokaci na Korona.

Share.

game da Author