Shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC ), a wa’adi na biyu don gudanar da aiki na tsawon shekara biyar.
An yi taron rantsarwar ne a jim kadan kafin a fara taron mako-mako na Majalisar Zartaswa ta Tarayya ta hanyar intanet a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
Idan kun tuna, tun a ranar 1 ga Disamba ne Majalisar Dattawa ta amince da sake nadin Yakubu a matsayin Shugaban na INEC.
Tabbatar da naɗin na Yakubu da majalisar ta yi ya biyo bayan rahoton da Kwamitin ta kan INEC, wanda Sanata Kabiru Gaya ke shugabanta, ya gabatar a lokacin zaman ta.
A ranar 25 ga Nuwamba ne Shugaba Buhari ya aika da sunan Yakubu ga Majalisar Dattawan domin ta amince da nadin sa a karo na biyu.
Buhari ya sake nada Yakubu ne a matsayin Shugaban INEC don gudanar da aikin shekara biyar a ranar 27 ga Oktoba.
Yakubu dai shi ne mutum na farko da zai jagoranci hukumar a karo biyu.
A jawabin da ya yi ga manema labarai da ke Fadar Shugaban Kasa bayan an rantsar da shi, Yakubu ya sha alwashin zai kara zage dantse wajen tabbatar da an rika gudanar da zabubbuka sahihai, kuma tsakani da Allah a kasar nan.
Ya nanata cewa INEC za ta ci gaba da hada gwiwa da Majalisar Tarayya wajen tabbatar da an yi wa dokokin zabe garambawul a cikin lokaci.
Ya ce: “A bayyane yake cewa mun nuna a zabubbukan da aka yi cikin ‘yan watannin nan cewa ana samun cigaba wajen shirya zabubbuka kuma za su ci gaba da inganta kamar yadda ya kamata.
“Majalisar Tarayya za ta shirya taron fadin albarkacin bakin ‘yan kasa a kan yi wa dokokin zabe garambawul.
“Wannan ya na da muhimmanci kuma a wannan karon, tare da hadin gwiwar Majalisar Tarayya, za mu tabbatar da cewa an zartar da kudirin garambawul din a cikin hanzari, kuma da zaran an yi hakan, zai taimaka mana kwarai da gaske wajen tunkarar dukkan kalubalen da ke gaban mu.
“An riga an yi nisa wajen shirye-shiryen zabubbukan shekara ta 2023; mu na bukatar tabbaci saboda haka hurumin dokokin zabe na da muhimmanci, wanda idan babu shi ba za mu iya fito da namu ƙa’idojin da dokokin ba.
“Idan babu namu ka’idojin da dokokin, ba za mu iya kammala aiki kan kundin horas da ma’aikatan wucin-gadi da za su yi aiki a lokutan zabubbukan ba.
“Saboda haka daga nan, zan tafi kai-tsaye zuwa Majalisar Tarayya ne, saboda a fara aiki gadan-gadan, wanda mun riga mun fara shi.’’
A taron na Majalisar Zartaswa ta Tarayya da aka yi ta hanyar intanet ya samu halartar Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, da Shugaban Ma’aikatan Ofishin Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, da Mai Bada Shawara Kan Harkokin Tsaro (NSA), Manjo-Janar Babagana Monguno (ritaya).
Sauran ‘yan majalisar da su ka halarci taron ido da ido sun hada da Antoni Janar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, da Ministan Yada Labarai Da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, da Ministan Ayyuka Da Gidaje, Babatunde Fashola, da Ministan Harkokin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika, da Ministar Harkokin Mata, Pauline Tallen, da Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji Da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouk, da sauran su.
Discussion about this post