Zababben Shugaban Kungiyar Daliban Jami’o’i ta Najeriya (NANS), Sunday Asefun, ya yi barazanar cewa za su rufe dukkan jami’o’i na kudi, wadanda ba na gwamnati ba, muddin aka kasa kawo karshen yajin aikin malaman jami’o’in gwamnati.
Watanni tara kenan malaman jami’o’i na ci gaba da yajin aikin neman biyan su yakkokin su sa su ka hada da alawus alawus da sauran hakkoki, sai kuma bukatar cika rubutaccen alkawarin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na gyara dakunan karatu da kara yawan su, ta yadda za a rage cinkoso a ajujuwa.
Lamarin ya kara muni yayin da Gwamnatin Tarayya ta umarci dukkan malaman jami’a su yi rajistar IPPIS, kafin a rika biyan su albashi.
An sha yin zaman tattaunawa tsakanin Kungiyar Malamai ta ASUU da Gwamnatin Tarayya. Na baya-bayan nan shi ne wanda Gwamnatin Tarayya ta amince za ta sauke lodin biyan kudaden alawus din malamai. Sai dai kuma har yanzu bangarorin biyu ba su daina sa-toka-sa-katsi a tsakanin su ba.
Sabon shugaban ya nuna jimamin irin zaman kuncin da daliban jami’a ke ci gaba da yi a gida. Ya ce duk wadanda su ka biya hayar dakuna a farkon shekarar nan, to ga shi shekarar ta kare, amma su na zaune a gidajen iyayen su.
Ya ce kuma ya na tausayawa ga daliban da ke hada gudu da susar duwawu, masu saye da sayarwa cikin jami’o’i.
“Yanzu dai ana fagen tuntuba da zama teburin shawararwari. Amma idan abin ya ci tura, to za mu kulle dukkan sauran jami’o’i na kudi wadanda su ba su yajin aiki.” Inji shi.
Kwanaki uku bayan Buhari ya gabatar da Kasafin 2021 cikin watan Oktoba, Gwamnatin Tarayya ta nanata cewa duk malamin jami’ar da ba ya cikin rajista nan da Nuwamba, zai yi asarar albashin sa.
Gwamnatin Tarayya ta sake yi wa malaman Jami’o’in Gwamnatin Tarayya gargadin cewa ta ba su wa’adin nan da watan Nuwamba kowa ya yi rajista da tsarin tantance karbar albashi na IPPIS ko kuma su yi asarar albashin su.
Wata sanarwar wasika da aka aika wa dukkan Shugabannin Jami’o’in Gwamnatin Tarayya (VC), an umarce su da su kara sanar da malaman cewa za a cire sunan duk wanda bai yi rajista da IPPIS ba daga tsarin biyan albashi.
Takardar wacce Daraktan Tsarin IPPIS na Ofishin Akanta Janar na Najeriya, Nsikak Ben ya sa wa hannu, ta ce duk malamin jami’ar da “bai samu yin rajista ta IPPIS ba, saboda dalilin ya tafi hutu, ko zaman jiyya asibiti ko haihuwa kuma bai samu damar yin rajistar IPPIS to ya gaggauta yi zuwa Nuwamba.
“Idan Nuwamba ta yi bai yi rajista ta, zai rasa albashin sa, har sai ya je Ofishin IPPIS a Ofishin Akanta Janar, tare da fam mai dauke da shaidar Shugaban Makaranta sannan a amince da shi.
“Sannan kuma sai ya hada da kwafen takardar shaidar karbar albashi na akalla watanni shida baya.” Inji sanarwar.
Ko a jawabin sa na gabatar da Kasafin Kudaden 2021, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi gargadin lallai sai malamin jami’a ya ‘rataya layar IPPIS’ sannan za a biya shi albashi -Buhari.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba za a biya malaman jami’o’i ko wani ma’aikatacin Gwamnatin Tarayya albashi ba, har sai ya yi rajistar Lambar Tantance Sahihan Ma’aikatan Gwamnati (IPPIS) tukunna.
Buhari ya yi wannan gargadin ne a yayin da ya ke gabatar da kasafin kudin 2021 na naira bilyan 13.08 a gaban daukacin Sanatoci da Mambobin Majalisar Tarayya, ranar Alhamis a Majalisar Tarayya, Abuja.
Ya ce an kirkiro tsarin tantance ma’aikata sahihai ne wato IPPIS domin a hana satar kudi ta hanyar harkalla da zamba, hana biyan ma’aikatan bogi albashi da kuma daukar ma’aikata ana biyan su albashi ba da umarnin gwamnatin tarayya ba.
Wata da watanni kenan malaman jami’a na yajin aiki, saboda rigima da gwamnatin Buhari a kan tsarin IPPIS, wanda su ka ce ba za a yi masu rajistar IPPIS ba.
Yayin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASSU) ta ce babu ruwan ta da IPPIS, ta ce ta na da na ta tsarin tantance malamai daban.
Shugaban ASSU, Biodun Ogunyemi ya ce ba za su koma makaranta ba, duk kuwa umarnin a koma karatu da gwamnati ta bayar, bayan shafe watanni bakwai dalibai na zaune a gida.
Ogunyemi ya ce ba za su koma ba, domin akwai malaman da ke bin albashin wattanni hudu zuwa shida duk ba a biya su ba.
Ya ce har yanzu gwamnati ba ta kama aniyar magance matsalolin da su ka dabaibaye fannin ilmi a kasar nan ba.
Discussion about this post