Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ya maidan wa PREMIUM TIMES martani a fusace, dangane da labarin da jaridar ta buga cewa, a lokacin ya na Ministan Harkokin Wutar Lantarki, ko Makamashi a takaice, an karkatar da naira bilyan 4.6 a kan idon sa.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda aka rika kamfatar makudan kudade ana turawa asusun ajiyar manyan ma’aikata, har sai da kudin su ka kai naira bilyan 4.6, a jajibirin karshen shekarar 2019.
Sai dai kuma a cikin martanin da Fashola ya maida wa jaridar, wanda kai-tsaye kokawa ce ya kama da PREMIUM TIMES, maimakon ya lahanta jaridar da tulin hujjoji, sai ya kara burma wa cikin sa ruwa.
Fashola ya ce kawai bi-ta-da-kulli PREMIUM TIMES ke yi masa, domin ba ma’aikatar sa kadai ce ke biyan kudade kai-tsaye a aljihun ma’aikatan gwamnati ba.
Fashola wanda rikakken lauya ne, ya yi subul-da-baka, ya ce ba shi kadai ne ake yin haka a ma’aikatar sa. Ya manta cewa, Sashe na 713 cikin Kundi na 7 na Dokar Kudaden Gwamnati an haramta a kwashi kudin gwamnati a zuba asusun bankin ma’aikacin gwamnati da sunan za a yi aiki, ko biyan kudin wani aiki.
Sannan kuma tsarin TSA ya haramta karkasa kudaden wata ma’aikata ko Hukuma cikin asusu daban-daban.
Fashola ya ce kudaden da PREMIUM TIMES ke ta magana a kai, an biya su ne a asusun ma’aikatan saboda ba su cikin sabon tsarin biyan kudi na IPPIS.
Sai dai kuma Fashola bai bayyana yadda aka yi da kudaden ba, kuma bai bada sunayen wadanda aka tura wa kudaden ba.
Sannan kuma PREMIUM TMES ta gano cewa dukkan ma’aikatan su na cikin tsarin IPPIS. in banda sabbin dauka. Wadanda aka tuttura wa kudade makudai kuma duk manyan ma’aikata ne, irin irin Darakta, Mataimakin Darakta, sai kuma gaggan wadanda su ka san kan tsiyar yadda ake nunke kudi baibai a ma’aikatun gwamnati.
Sannan kuma Fashola ya kantara karya da ya ce wadanda aka tura wa kudaden ba su cikin IPPIS, domin kudaden ba ma na tafiyar da ayyukan yau da kullum ba ne, duk na manyan ayyuka ne, wadanda babu wani dalilin da zai sa kudin su shiga aljifan ma’aikatar gwamnati, domin su ba ‘yan kwangila ba ne.
Sannan kuma inda aka bar Fashola kan kwana, bai san cewa Daraktan Harkokin Kudade na Ma’aikatar Lantarki, wanda a yanzu ba a karkashin Fashola din ta ke ba, mai suna Omotayo Adewumi, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa kudaden ba a asusun wadanda ba su kan tsarin IPPIS aka tura su ba. Cewa ya yi an tura su a asusun wadanda ba su kan tsarin tantancewa da bin diddigin kudaden kasafin kudi na GIFMIS.
Fashola ya amince cewa “wadannan kudade da aka biya ta hanyar da PREMIUM TIMES ta fallasa, sun zama abin damuwa ga wasu hukumomin da ke sa-ido kan kudade.
Cikin raddin da Fashola ya yi wa PREMIUM TIMES, inda ya kira rahoton da ta fallasa da “SHASHANCI”, Minista ya ce Mimista ba shi da masaniyar yadda Daraktocin Kudade a Ma’aikatu ke biyan kudade, domin ba a karkashin Minista su ke ba, duk su na karkashin Ofishin Akanta Janar na Tarayya ne, domin daga can ake tura su.
Sai dai kuma wani babban jami’i a Ofishin Akanta Janar, ya ce karya Fashola ke yi.
“Kawai Minista na borin-kunya ne. Tunda aka rigaya aka fito da tsarin TSA, babu wani dalili da zai sa a rika zuba kudaden gwamnati a asusun ma’aikatan gwamnati, sai fa dama idan an shirya karkatar da kudaden ne kawai.”
Jami’in ya nemi a sakaya sunan sa, kuma ya ce kamata ya yi EFCC da ICPC su binciki su Fashola.
Wanda Ya Raba Fada Bai Kallo Ba: Asalin Dalilin Kokawa Tsakanin Fashola Da PREMIUM TIMES:
Farkon makon da ya gabata ne PREMIUM TIMES ta buga labari mai take: TONON SILILI: Yadda ma’aikatar Fashola ta kacaccala wa ma’aikatan ta naira bilyan 4.6, kowa ya yi gum da bakin sa.
Tsakanin watan Satumba zuwa Disamba na 2019, an sungumi zunzurutun naira bilyan 4.6 na Ma’aikatar Makamashi, Ayyuka da Gidaje aka rika gabza ana tutturawa asusun ajiyar banki na wasu daraktoci da ma’aikatan da ke ma’aikatun uku.
PREMIUM TIMES ta tabbatar da haka a wani binciken kwakwaf da ta yi. Kuma ta mallaki takardun da su ka tabbatar da cewa tuttura kudaden duk harkalla ce.
PREMIUM TIMES ta tura wa Ma’aikatar Makamashi, wato hasken lantanki wasikar neman rekod din kidaden da aka tura. Amma sai aka amsa da cewa naira milyan 157 ne kadai aka tura a Asus use mutane 127.
Sai dai kuma kwafe-kwafen takardun bayanan sa ke hannun PREMIUM TIMES, ya tabbatar ce karya ma’aikatar ke yi.
A yanzu dai Ma’aikatar Makamashi ita kadai ta ke, an cire ta karkashin rukunin ma’aikatun da ke karkashin Minista Raji Fashola, aka nada mata Minista Sale Mamman.
Amma dai a lokacin da aka gabji makudan kudaden aka yi watanda da su, ma’aikatar makamashi wato lantarki, a hannun Fashola ta ke.
Yadda Mutum 21 Su Ka Jide Naira Bilyan 4.6:
Rekod din da PREMIUM TIMES ta samu a Rumbun Tattara Bayanan Kidade (Open Treasury Portal), ya nuna cewa an daddatsa kudaden har gida 654, duk aka tura cikin asusun mutum 21.
Kashi 2 bisa 3 na kidaden duk mutum 2 aka tura wa su: Ogueri Ugochukwu Pascal da wani mai suna Olasehinde Micah.
An loda naira bilyan 1.6 asusun Pascal (N1,642,4407,539.93). Ba lokaci daya aka gabza masa kudin ba. Daddatsa kudin aka yi, aka rika tura masa har su 306.
Shi ma Micah an tura masa naira bilyan 1.4 (1,417,921,892.59). Shi kuma sau 34 aka tura masa kudaden.
Akasarin kudaden an tura su ne tare da bayanan abin da aka yi da kudaden. Amma bayanan daga na bige, gidoga sai na bad-da-bami.
Misali: An tura wa Pascal naira milyan 157 a ranar 26 Ga Oktoba, sai aka rubuta cewa kudin “rangadin neman kudin shiga ne na shiyya” da sauran dalilai da aka rubuta na logar Turanci mai kumbura wa mai karatu kai, yadda zai ga kamar wani gagarimin aiki ne aka yi da kudaden.
An danna naira milyan asusun wani mai suna Kamaru, har milyan 134.
PREMIUM TIMES ta kasa gano ko au wane ne Pascal da Kamoru.
Wasu da su ka samu na su rabon wannan watanda, sun hada Onwubalili Oyinlola, Nwaimo Obi Valenrine, Uzodinma Lucy Iquo; Oko Jaja Emmanuel, Waziri Mishella Micah. Kuma yawancin su duk daraktoci ne.
Akwai kuma jerin sunayen mutanen da aka kacalla wa kudaden, cikin su har da mai naira 583,200, wata mai suna Nafisa Yaro Ahmed.
Karya Dokar Hana Kudi Shiga Aljihun Ma’aikaci:
Abin da aka yi ya karya sashen Dokar Hada-hadar Kudade ta 7, Sashe na 701. Sannan kuma Doka Sashe na 713 ta jaddada kada a kuskura a yi haka, wato a kwashi kudin gwamnati a tura asusun ma’aikacin gwamnati.
An kuma gano an dankara wa wata mata mai suna Aishatu Audu Jauro naira milyan 13.5 domin “horas da ma’aikata.”
An dai gano cewa a shekarar 2019 an biya kudsden gwamnati har naira bilyan 51 a cikin asusun daidaikun mutane, wanda haka babban laifi ne a dokar kasa.
Jimillar kudaden da aka tura wa jama’a, alhali dokar kasa ta haramta irin wannan biyan kudade, sun kai naira bilyan 278. An raba kudaden ga mutum 5,000. Ko kuma a ce an tura kudaden sau 5000.
Discussion about this post