GARKUWA DA MUTANE: Mahara sun kashe mutum biyu, sun ji wa wasu rauni a Kaduna

0

Mahara na cigaba da afkawa mutanen kauyukan jihar Kaduna musamman na karamar hukumar Igabi.

A daren Litinin, wasu mahara sun dira kauyen Maigiginya dake karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna, sun kashe mutum biyu kuma suka ji wa wasu da rauni.

Wadanda suka kashe suna Nasiru Yahaya da Isah Bature, su kuma Magaji Goma da Zulkarnaini Yahaya harbin su aka yi da bindiga amma basu mutu ba.

Maharan su kwashe wa jama’a abinci da duk wani abu da suka ci karo da shi.

Sai dai kuma kwamishinan Tsaron jaihar Kaduna da Samuel Aruwan ya ce maharan ba daga cikin wadanda aka fafura daga dajin Kaduna-Abuja wadanda suka addabi mahara.

Aruwan yace jami’an tsaro ne suka darkaki maharan dake wannan daji, shine suka arce kuma suka yada zango a karamar hukumar Igabi.

” Dakarun tsaro sun kai wa mahara hari a boyarsu a dazukan dake wannan titi. Gwamnati ba za ta daga kafa ba har sai an kawo karshen wadannan mahara.

Share.

game da Author