KORONA: Mutum 168 suka kamu a Najeriya ranar Talata

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 168 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Talata.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –50, FCT-61, Kaduna-27, Oyo-12, Rivers-6, Katsina-5, Ogun-3, Kwara-2, Edo-1, da Kano-1

Yanzu mutum 66,607 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 62,311 sun warke, 1,169 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 3,127 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 23,018, FCT –6,576, Oyo – 3,715, Edo –2,695, Delta –1,823, Rivers 2,963, Kano –1,777, Ogun –2,156, Kaduna –2,940, Katsina -1,012, Ondo –1,727, Borno –745, Gombe – 938, Bauchi – 753, Ebonyi –1,055, Filato -3,805, Enugu – 1,332, Abia – 926, Imo –662, Jigawa – 328, Kwara –1,095, Bayelsa – 445, Nasarawa – 485, Osun –945, Sokoto – 165, Niger – 296, Akwa Ibom – 319, Benue – 493, Adamawa – 261, Anambra – 282, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 94, Ekiti – 354, Taraba- 157, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.

Alkaluman da ‘Wordometer’ ta fitar ya nuna cewa mutum sama da 250,000 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar korona a kasar Amurka.

Alkaluman ya kuma nuna cewa kasar ta ci gaba da samun na hau-hawan yawan mutanen dake kamuwa da cutar da wadanda ke rasuwa a kullum.

A makon da ya gabata akalla mutum 1,167 suka mutu a cikin uni daya.

A yanzu dai Amurka ita ce kan gaba wajen samun yawan mutanen da korona ta kashe a duniya.

Mutum miliyan 11.8 me suka mutu a Amurka a yanzu haka.

A yanzu mutum miliyan 56 ne suka kamu da cutar sannan miliyan 1.3 sun mutu a duniya.

Share.

game da Author