Mahara sun dira Kwatas din jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, a cikin daren Lahadi in da suka yi garkuwa da malamin makarantan, matarsa da diyar sa.
Darektan Hulda da Jama’a na Jami’ar Auwalu Umar, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wani takarda da ya saka wa hannu ranar Litinin.
Yace mahara sun afka gidan wannan malami da ke kwatas din jami’ar suka yi awon gaba da shi.
” Maharan sun yi awon gaba da malamin da iyalansa ne, sai dai daga baya sun sake su bayan jami’an tsaro sun bi sawun su sai suka saki matar malamin da yarsa.
“Da misalin karfe 12:50 na safiyar ranar Litinin, 23 ga Nuwamba, 2020, maharan suka afkawa gidan wani ma’aikacin jami’ar da ke kan titin Sardauna, a kwatas din Samaru, Zariya. Sun arce da shi da matarsa da ‘yarsa.
Idan ba a manta ba ko awa 24 ba a yi ba da sako wasu daliban jami’ar ABU da mahara suka yi.