Saboda tsananin kishi wata budurwa mai suna Jamila Ibrahim ta babbake gidan tsohon saurayinta Mohammed Yusuf dake Unguwar Festac jihar Legas.
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta bayyana cewa ta tsare Jamila Ibrahim da wata kawarta Fatima Mohammed da a ke zargi da babbake gidan tsohon saurayi mai suna Mohammed Yusuf dake unguwar Festac, a jihar Legas.
Ko da Yusuf ya isa gidan sa da ‘yan matan suka banka wa wuta yayi kokarin fidda sabuwar budurwarsa mai suna Rabi. Duk da ya yi kokarin fiddata Allah yayi mata cikawa bayan ya kaita asibiti.
Ita fatima ‘yar rakiyace kuma kawar Jamila.
Yanzu dai suna nan tsare a ofishin ‘yan sanda ana cigaba da bincike.
Discussion about this post