Korona ta karya tattalin Arzikin Najeriya – Buhari

0

Yayin da Najeriya ta fada cikin koma bayan tattalin arziki a karo na biyu a cikin shekaru biyar, Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce hakan ya faru ne saboda tsananin tabarbarewar tattalin arzikin duniya da annobar Korona ta haifar.

Shugaba Buhari fadi haka ne a ranar Litinin a Abuja a wajen bude taron koli na tattalin arzikin Najeriya karo na 26 mai taken: ” Gina kawancen don juriya”.

Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Najeriya (NESG) da Ma’aikatar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-tsaren kasa ne suka shirya taron.

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ne ya wakilci shugaba Buhari a wajen taron.

Ya ce koma bayan da aka samu ya yiwune a sanadiyyar Garkame iyakokin kasashe da aka yi, babu shiga babu fita sannan babu hada-hadar cinikayya da kasuwanci sannan kuma da rashin aikin yi da aka yi fama da shi.

” Zamu iya tuna cewa a lokacin da ake zaman kulle saboda Korona, ayyukan noma ya tsaya cak, kasuwanni sun kasance a rufe haka makarantu. Suma otel-otel da gidajen abinci duk sun kasance a garkame.

“Hakanan, kamfanonin jiragen sama sun daina zirga-zirgar da jigilar fasinjoji, a takaice dai komai ya tsaya cak.

Ministar Harakokin Kudi, Zainab Ahmed, ta ce koma bayan tattalin arzikin da aka fada yanzu zai zama dan gajeren lokaci, saboda gwamnati da manyan masu ruwa da tsaki suna aiki kafada da kafada don tsarawa da samar da matakai masu dorewa don takaitawa da inganta yanayin cikin gaggawa.

Zainab ta kara da cewa duk da ruftawa da Najeriya ta yi na karayar tattalin arziki, tattalin Arzikin kasar ya zarce na kasashe da dama.

A karshe shugaban Kungiyar NESG Asue Ighodalo, yayi kira ga attaijira masu kamfanoni masu zaman kansu wato mambobin wannan kungiya da su yi hubbasa wajen ganin an samu canji ba kawai a tsaya kullum sai dai ayi ta karance karance ba.

Share.

game da Author