KILU TA JA BAU: Kotu ta ce a tsare Ndume a Kurkukun Kuje saboda Maina

0

Babban Kotun Tarayya a Abuja, ta umarci jami’an tsaro su garkame Ali Ndume a kurkukun Kuje har sai Abdulrasheed Maina ya kawo kan sa Kotu, ko kuma shi da kansa ya bayyana.

Alkalin Kotun Okon Abang, ya yanke hukuncin cewa, Ndume da da damar ya bayyana da lauyoyin sa ranar 23 ga Disemba, ranar da za a ci gaba da sauraren karan.

Lauyan EFCC ya roki kotu ta tilasta wa Ndume ya mika jinginan kadaran da aka yi sannan kuma a cafke Ndume tunda shine ya tsaya masa.

Na nemi Maina na rasa, bayan na karbi belin sa -Inji Sanata Ndume a kotu

Sanata Ali Ndume ya shaida wa Babbar Kotun Tarayya a Abuja cewa, ya nemi tsohon Shugaban Kwamitin Kwatar Ƙuɗaɗen Fansho, Abdulrashid Maina, amma ya rasa inda ya ke.

Ndume ya yi wannan bayanin a matsayin sa na wanda ya tsaya a kotu ya karɓi belin Maina, bayan ya shafe watanni bakwai a kurkuku saboda ya rasa mai beli.

An zargi Maina da karkatar da naira bilyan 100 na kudaden fansho. Sannan kuma ana zargin sa da laifin karkatar da kudade ta bahaguwar hanya, wato money laundering.’

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da shi a Babbar Kotun Tarayya, inda ta tuhume shi da aikata laifuka 13, ciki har da bude asusun ajiyar kidade na harkalla da kuma aika ayyukan zamba.

Jami’an SSS ne su ka damke shi cikin 2019, bayan ya shafe shekara daya cur ya na wasan-buya da jamii tsaro.

SSS sun damka shi a hannun EFCC, su kuma su ka gurfanar da shi kotu.

PREMIUM TIMES ta buga albarin yadda Sanata Ndume ya amince ya karbi belin Maina, bayan ya shafe watanni a tsaye, ya rasa mai belin sa.

Kotu: Yayin da Mai Shari’a ya nemi jin ta bakin Ndume, saboda a cikin sati sau uku ana umartar sa ya gabatar da Maina a kotu, amma abin ya gagara, Ndume a wannan karo ya ce ya nemi Maina sama ko kasa, amma ya rasa inda ya ke.

Tun da farko Mai Shari’a Abang Okon ya nemi Ndume ya kai Maina kotu a matsayin musayar kuɗin belin da ya ajiye.

Da farko an nemi sai an ajiye naira bilyan daya za a bayar da belin Maina, sai kuma mutum daya mai tsaya masa.

Daga baya saboda an rasa mai beli, alkali ya amince a ajiye takardun kadarorin da suka kai naira milyan 500 a Abuja, wanda Ndume ya bayar din aka ba shi belin Maina.

Ran Mai Shari’a ya baci matuka, inda a karshe ya ce tilas a ranar 5 Ga Oktoba, Ndume ya kai Maina a kotu, ko ana ha-maza-ha-mata.

Share.

game da Author