HIMMA MANOMA: Yadda ake nuna min bambanci wajen cin gajiyar noma, saboda ina mace -Aji Washuku

0

Wanda ya yi arba da Aji Washuku, wata mai harkokin noma a kauyen su a Jihar Taraba, zai yarda da kididdigar da Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) da kuma Ma’aikatar Ayyukan Gona ta Kasa su ka yi cewa, kashi 75 na kananan manoman da ake kai kayan abincin da su ke nomawa a kasuwa, duk mata ne.

Ita dai Washuku mai shekaru 56, ta na da ‘ya’ya hudu, a wata tattaunawa da PREMIUM TIMES, ta bayyana irin gwagwarmaya, fadi-tashi da kuma abin da ta kira bambancin da ake nuna mata a harkar noma, saboda kawai ita mace ce.

Ta fara da bada labarin irin kayan gonar da ta ke nomawa, wadanda su ka hada da dankalin Turawa, shinkafa, yakuwa (zoborodo), waken soya da masara.

Washuku, wadda ta ce ta shafe shekaru 20 ta na harkokin noma, ta ce ta na da gonar ta ta kan ta, amma saboda noman na ta ya fara karfi, sai ta rika karbar jingina ko noma-tashi a wadansu wurare.

“Amma zuwa yanzu ina yin noma a gonaki biyar. Akwai mai fadin hekta 1, akwai mai hekta 2 da mai hekta 3.

Washushu ba ido-rufe ta ta ke noman ta ba. Ta ce a Cibiyar Bincike da Bunkasa Harkokin Noma ta Zaria ta ke sayo irin da ta ke shukawa.

Ta ce ta kuma san akwai irin da ake samu daga Hukumar Bunkasa Noma (ADP) a Taraba.

Duk da ta ce ta kan yi amfani da irin ADP, Washushu ta ce har yau ba ta taba amfani da injinan zamani wajen noman ta ba.

Cewa ta yi ita ai mai karamin karfi ce, ba ta iya biyan kudi ta karbi hayar injinan bunkasa noma. Saboda haka duk da hannu ake yi mata noma.

“Na kan noma shinkafa buhu 30 mai nauyin kilo 100, masara buhu 20 mai nauyin kilo 100. Sauran kuma na kan noma buhu 5 zuwa 10 masu nauyin kilo 100 kowanen su.

An tambaye ta yadda ta ke adana amfanin gona. Sai Washushu ta ce akwai wani buhu na musamman da ake samu a wajen ADP a Taraba, ya na da leda har nunki biyu a cikin sa. To da shi ake adana anfanin gonar.

Sannan kuma ta ce yawancin kayan noman na ta sayarwa ta ke yi, amma ta kan rage kadan ta rika ci a gida.

Ta ce ba kasuwa ta ke kaiwa ba. Akwai wasu masu sayen amfanin gona da ke zuwa lokacin kaka su na saye a hannun su. Amma dai harkar inji ta, ba ta samun kwarin-guiwa ko karfafawa.

Ta ce idan ba a zo an saya duka ba, ta kan sayar ta taimaka wa mijin ta wajen dawainiyar tafiyar da gida, sai kuma kula da karatun yaran su hudu.

Wadanda su ka rage kuma ta kan kimshe a cikin buhunan ADP, domin idan aka adana a cikin buhunan, su kan shekara biyu zuwa uku ba su rube ba.

Ta ce ba ta samun tallafi daga gwamnati. An dai taba ba su irin shinkafa, shi ma akwai-ya-babu ne, domin bai ishe ta ba.

Haka tallafin korona na Covid 19 da aka raba, Washuku ta ce ta na ji ta na gani aka raba, amma ba ta samu ba.

“An kawo kayan noma na na’urori amma saboda maza sun yi mana kaka-gida, sai su ka rabe a junan su, babu wata mace ko guda daya da ta samu.”

Share.

game da Author