Wata mata da ta maida himma wajen ayyukan noma a cikin karkara a Jihar Kaduna, mai suna Hannatu Soni, ta ce duk da ba ta samun tallafin gwamnati wajen bunkasa noma, hakan bai hana ta samun lidifi da nasibi da albarkar noma ba.
“Sai ka ji ana cewa an raba wa mata tallafin noma. To ni dai ban san irin matan da su ke magana a kai ba.”
Hannatu manomiya ce a jihar Kaduna, kuma ta na da ‘ya’ya biyar. Mai shekara 59. Ta bayyana cewa banda noman damina da ta ke yi, da rani kuma ta na noma tumatir da barkono. Da damina kuma ta na noma masara, shinkafa dawa.
A tsawon shekaru 30 da ta ce ta na harkar noma, ta ce da farko hayar gonaki ta kan rika karba kadai. Amma lokacin da mijin ta ya ci gadon wasu gonaki, sai ta rika noma wasu gonaki da mijin Ya ci gado.
Ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa wadda ta ke karba haya ta kai hekta 10. Ta mijin ta kuma da ta ke nomawa za ta kai hekta 9.5. Sannan kuma akwai wata mai fadin hekta 3.
Hannatu ta ce ta shafe shekaru ta na samun iri a gargajiyance. Amma da su ka samu horaswa, sai su ka rika samun irin shuka daga gwamnatin jihar Kaduna.
Sai dai kuma ta ce wannan duk tarihi ne, domin yanzu ba su samun tallafin komai daga gwamnatin Kaduna.
“Amma yanzu na yi gam-da-katar da wani kamfani da ya ke ba ni iri ina shuka masa, ya na biya na. To kuma daga nan ni ma na ke samun nawa irin ina shukawa.”
Ta ce wannan tsarin da ta ke yi tare da kamfanin, na irin masara ne kawai.
Hannatu ta ce ta na yin amfani da noman zamani a gonakin ta masu girma da fadi. Amma a kananan, noman hannu ake yi.
Ta ce amma haya su ke dauko motar tarakta domin a yi masu haro, duk hekta daya a kan naira 25,000.
Ta ce ruwan sama mai karfi a wannan shekara ya janyo mata asara sosai.
Ta ce ta na adana kayan noma a cikin buhunna, ta sayar da wasu, wasu kuma a ci a gida. Amma ta ce a kasuwannin kauyuka ake kai amfanin gonar ana sayarwa.
Hannatu ta ce ta na kashe kudin cinikin wajen biyan kudin makaranta, domin mijin ta ba ya iya komai, saboda rashin lafiya ta kwantar da shi.
“Ba ni samun tallafin komai daga gwamnati. Wasu gungun mata dai sun sayi taki akan buhu naira 5,000. Amma ni buhu biyu kadai na samu.
“Lokacin da aka kaddamar da shirin noma na shekarar 2020 a Jihar Kaduna, sai aka bai wa mata manoma su dubu goma sunkin buhun irin shuka 20 kacal. To buhun masara 20 me zai yi wa manomi dubu goma?
“Ni da abin ya bata min rai ma, barin wurin na yi, na ce wa wata idan ta na bukatar nawa kason, to tsaya ta karba, na bar mata.”