Najeriya ta karbi dala bilyan 26.9 matsayin tallafi daga kasashen waje cikin shekaru shida – Ministan Kudi

0

Karamin Ministan Harkokin Kudade, Clement Agba, ya bayyana cewa tsakanin 2015 zuwa 2020, Najeriya ta karbi taimako na kudade daga kungiyoyi da cibiyoyin kasasshen duniya har dala bilyan 26.94

Agba ya yi wannan karin hasken ranar Talata a Abuja, lokacin da ya ke yi wa Kwamitin Majalisar Tarayya bayani a kan adadin kudaden da aka bi wa Najeriya taimako, agaji da tallafi daga kasashen waje.

“Cikin 2015 an karbi dala bilyan 2.34; sai dala bilyan 1.15 cikin cikin 2016. Shekara ta gaba, wato 2917 kuwa, dala milyan 774.93.

Cikin 2018 an karbo dala bilyan 22.03. Sai a 2019 aka karbo dala milyan 655.64. Cikin 2020 kuwa, dala milyan 5.64 kadai aka karbo.

Agba ya ce wadanann kudaden sun fito daga Gidauniyar Turai ta EDF da kuma UNDS, da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya (UN).

Ya kara da cewa wasu kudaden kuma sun fito daga kasar Chana, bisa alkawarin da aka yi tsakanin kasashen biyu tun cikin 1972.

Ya ce akwai wasu daga Japan da Koriya da kuma DFID da USAID Cibiyar GIZ ta kasar Jamus.

Agba ya Ma’aikatar Harkokin Kudade ba ita ke karbar kudaden ba. Shi ya sa ba ta iya tura wa wata hukuma ko ma’aikata ko sisi daga cikin kudaden.

Ya ce a yanzu kuma Najeriya ba ta iya samun tallafi ko na sisi domin kara wa kasafin kudi nauyi, saboda duniya ta daina saka ta a jerin kasashen da ke fama da fatara da talauci.

Ya ce yanzu masu bada tallafin kudaden ba su bai wa gwamnatin tarayya kai-tsaye. Sai dai su bi diddigin inda za a yi wa al’umma aiki, a nuna masu, su yi musu aikin kai-tsaye.

Share.

game da Author