TALLAFI: Gwamnatin Tarayya ta raba naira bilyan 6 ga matan karkarar Zamfara su 2,800 – Minista Sadiya

0

Gwamnatin Tarayya ta ba matan karkara 2,800 agajin kudi N20,000 kowaccen su a Jihar Zamfara a Shirin Bada Tallafin Kudi ga Matan Karkara, wato ‘Grant Project for Rural Women’.

Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta kaddamar da tsarin biyan kudin, wanda sau daya ake biya, a Gusau a ranar Talata.

A taron, ministar ta bayyana cewa rabon kudin wani ɓangare ne na kokarin da Shugaba Muhammadu Buhari ya ke yi na cika alkawarin gwamnatin sa na magance matsalolin rayuwar jama’a.

Ta ce, “An fito da shirin bada tallafin kudi ga matan karkara ne (Grant for Rural Women programme) domin a cika alkawarin gwamnatin Buhari na magance matsalolin al’umma, wanda ya haɗa da muradin ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin fatara da yunwa nan da shekaru 10 masu zuwa.

“An tsara shi domin a samar da hanyar fara bada tallafin kudi ga wasu daga cikin matan karkara da su ka fi shan wahala a Najeriya.

Kananan Hukumomin Anka, Tsafe, Talata Mafara, Bungudu, Kaura Namoda da Birnin Magaji ne su ka fara cin moriyar shirin.

“Za a riƙa bada kuɗi N20,000.00 ga kowace daga cikin matan karkara mabukata sama da 150,000 a dukkan jihohi 36 na kasar nan da kuma Yankin Birnin Tarayya.

“Ana sa ran tallafin kudin zai ba mata dama su samu jarin kudi da za su yi sana’o’i. Fatar mu ita ce wadanda su ka ci moriyar wannan shiri za su yi amfani da wannan damar wajen kara hanyoyin samun kudin shiga, da ƙara samun abinci da kuma uwa-uba inganta rayuwar su ta yau da kullum.”

Daya daga cikin matan da aka ba tallafin kudi N20,000, Malama A’isha, wadda ‘yar shekara 80 ce, ta bayyana jin dadin ta kan yadda aka yi rabon, kuma ta gode wa Shugaba Buhari saboda ya tuno da matalauta a wannan mawuyacin hali da ake ciki.

Mata 200 daga kowace daga cikin kananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara ne za a ba tallafin N20,000 kowaccen su.

Gwamnatin Buhari ta fito da shirin a cikin 2016, domin inganta rayuwar marasa galihu, ta hanyar cike gurabun ratar da aka yi masu, wajen samun karfi da galihun dogaro da kan su cikin al’umma.

Share.

game da Author