Dubban mazauna garin Abuja basu iya isa gidajen su a daren Juma’a a dalilin daddatse manyan titunan garin da masu zanga-zangar #EndSARS suka yi.
Hakan yasa da a lama dai wasu da dama za su yi kwanan titi ne.
Masu zanga-zangar EndSARS sun ce ba za su daina zanga-zanga ba duk da Buhari ya rusa rundunar SARS din da kuma aiwatar da wasu dokoki domin kawo sauyi da inganta rundunar ‘yan sandan.
Musamman a jihohin Kudancin Kasar nan, abin sai kara kazanta yake yi.
PREMIUM TIMES ta kawo rahonton yadda wasu da ake zargin zauna-gari-banza ne, su ka kai wa masu zanga-zangar #EndSARS farmaki, har su ka ragargaza motoci biyar.
An shiga rana ta 10 ana zanga-zanga a Abuja. Masu zanga-zanga sun yi dandazo a Gadar Berger, su na kururuwar a sauya fasalin aikin ‘yan sanda.
Sun fara lafiya kalau amma wajen karfe 1 na rana sai wasu ‘yan daba dauke da sanduna da falankan katako su ka nemi tarwatsa su.
Sun rika lalata motocin da masu zanga-zanga su ajiye a gefen titi, kuma su na kai wa ‘yan #EndSARS hari.
Ana ci gaba da zanga-zanga duk kuwa da an rushe SARS, kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya sa a yi bincike, a gurfanar da jami’an da su ka wuce gona-da-iri, su ka rik yake hakkin jama’a.