Masu satar bayanai da kutsen shafukan yanar gizo sun dira wa shafin Babban Bankin Najeriya, CBN sun garkame ta

0

Kwanaki biyu bayan sun kwace shafin intanet na Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya (NPF) da na Hukumar Kula da Gidajen Radiyo da Talbijin ta Najeriya (NBC), yanzu kuma gaggan kadangarun bariki na duniya masu shigar-kutse shafukan intanet, sun kutsa shafin babban bankin Najeriya.

Wadannan gungun mashahuran-boye, kuma gaggan kadangarun barikin tashoshin intanet na duniya, sun yi sanarwa a ranar Juma’a cewa sun ci gaba da nuna goyon bayan zanga-zangar #EndSARS, ta hanyar kwace wasu shafukan mallakin gwamnatin Najeriya ciki har da CBN.

Yanzu haka shafin baya buduwa kwata-kwata.

Abin dai a hankali yana neman ya kazanta domin hatta mutanen Abuja sun kasa komawa gidajen su saboda daddatse tituna da masu zanga-zangar #EndSars suka yi.

PREMIUM TIMES a ranar Alhamis ta bada labarin yadda Gaggan ‘yan buruntu sun kutsa cikin rumbun bayanan sirrin ‘Yan Najeriya na intanet.

An kasa shiga rumbun tattara bayanan Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya bayan da wasu gaggan kadangarun bariki masu shigar-kutse a shafukan intanet din hukumomin gwamnati sun kwace shafin.

Dama kuma wadannan masu shigar-kutse da su ka yi kaurin suna a duniya, sun bayyana karara cewa za su kutsa cikin shafukan intanet din hukumomin gwamnati, domin nuna goyon bayan su ga zanga-zangar #EndSARS, ‘yan sandan da sunan su ya baci wajen gallaza wa wadanda ba su ji ba, ba su kuma gani ba.

Wadannan gungun masu shigar-kutse a shafukan intanet, wato “hacktivists” wato ‘yan-a-kutsa, babu wanda zai ce ga ko su wane ne, saboda komai a asirce su ke yi.

Sai ma da su ka yi sanarwa a shafin su na Twitter cewa za su kutsa cikin shafukan hukumomin gwamnati. Kuma su na da mabiya a Twitter sama da mutum milyan biyar.

Kafin su kutsa cikin shafin bayanan Rundunar ‘Yan Sanda, sai da su ka yi sanarwar nuna goyon bayan zanga-zangar neman a rushe SARS.

Bayan ta kutsa kuma sai su ka saki sunayen da bayanan jami’an ‘yan sanda, adireshin su da lambobin asusun ajiyar su a bankuna.

Duk kokarin shiga shafin intanet din ya gagara, saboda ‘yan kutse sun kwace shi.

Kafin buga labarin an kasa samun kakakin yada labarai na ‘yan sanda domin karin bayani.

Sun taba yin irin wadannan kutse a Amurka, Israila, Tunisiya, Uganda da wasu kasashe.

Share.

game da Author