#EndSARS: Ina rokon matasan Najeriya su yi hakuri su maida wukaken – Osinbajo

0

Mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya yi kira ga ‘yan Najeriya da masu zanga-zanga musamman matasa da su yi hakuri su ba gwamnati dama su cigaba da kokarin kawo sauye-sauye da take yi.

Osinbajo wanda ya rubuta haka a shafin sa ta Tiwita ya ce baya ga rusa rundunar SARS da gwamnati tayi, vba za a nada ko da mutum daya bane wanda ya taba aiki a karkashin rundunar SARS a Najeriya.

” Na sani lallai mun yi shiru na tsawon lokaci bamu ce komai, ku yi mana afuwa duk da dai hakan ba hujja bane da gwamnati za ta yi tunkaho da.

” Lallai akwai mutane da yawa da ‘yan sanda suka ci wa mutunci babu gauira babu dalili a kasar nan musammam matasa. Hakan bai dace kuma ba za a kyale shikenan an bar maganan ba. Wanda kuma ana biyan su ne domin kare su.

” Gwamnati na bibiyar yadda zanga-zangar ke gudana kuma ina tabbatar muku da ni da shugaban Kasa da Shugaban Majalisun Tarayya suk muna tsaye ne don ganin an kawo karshen wannan matsala. Sanna kuma gwamnatin Tarayya ta umarci gwamnatocin jihohi da su kafa kwamitocin domin duba matsalar da aka samu da ‘yan sanda kan cin cin mutuncin mutane da suke yi da cin zarafin su domin a hukuntasu.

Bayan haka kuma gwamnati ta umarci gwamnoni su kafa wata asusun musamman da za a biya diyyar wadanda aka kashe da wadanda aka ci zarafin su.

Share.

game da Author